Dino Melaye: Da kansa ya bude kofar gidan yau - Yan sanda

Dino Melaye: Da kansa ya bude kofar gidan yau - Yan sanda

Sanata mai wakiltan mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye, na hannun jami'an yaki da yan fashi da masu garkuwa da mutane wato FSARS, wata majiya a hedkwatan yan sanda ta tabbatar da hakan.

Jami'an yan sandan sun gudanar da bincike cikin gidansa yayinda aka kaishi ofishin hukumar FSARS dake Guzape, birnin tarayya Abuja.

Duk da cewa a baya Sanatan ya bayyana cewa ba ya cikin gidan da yan sanda suka mamaye na tsawon kwanaki takwas, jami'an yan sandan sunce shi ya bude kofar gidan da kan misalin karfe 3 na ranan Juma'a, 4 ga watan Junairu, 2019.

Da ya fito daga gidan, sai ya fadi warwas a kasa kama wani mara lafiya gaban wasu yan majalisan jam'iyyar PDP da yan sanda.

Daga baya sai aka shigar da shi cikin motarsa aka tafi da shi ofishin yan sandan.

Mun kawo muku rahoton cewa Bayan kwanaki takwas da zaman din-din-din da jami'an yan sanda sukayi a kofar gidan dan majalisar dattawan Najeriya mai wakilta Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye, ya mika wuya ga hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel