Jam’iyyu 91 sun nemi INEC ta tsige Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin zabe

Jam’iyyu 91 sun nemi INEC ta tsige Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin zabe

- Jam’iyyun siyasa 91 da aka yi wa rijita a karkashin kungiyar IPAC sun nemi INEC da ta yi gaggawan janye nadin da ta yi wa Amina Zakari

- An dai nada Amina ne a matsayin shugabar kwamitin sanar da sakamakon zabe a jiya Alhamis

- Jam’iyyun na adawa da wannan nadin ne kasancewarta yar’uwa ga shugaba Buhari

Jam’iyyun siyasa 91 da aka yi wa rijita a karkashin kungiyar Inter-Party Advisory Council sun yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta yi gaggawan janye nadin da ta yi wa Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin sanar da sakamakon zabe.

IPAC wata kungiya ce da INEC ta amincewa kuma ta ke magana a madadin dukkanin jam’iyyun siyasa a kasar.

Jam’iyyu 91 sun nemi INEC ta tsige Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin zabe

Jam’iyyu 91 sun nemi INEC ta tsige Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin zabe
Source: Twitter

Jam’iyyun siyasa hudu ciki harda babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressive Grand Alliance (APGA) a ranar Alhamis sun nemi a tsige Zakari wacce suke ganin yar’uwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta jini ce.

Da yake magana da majiyarmu a ranar Juma’a, shugaban IPAC, Mista Peter Ameh ya nemi INEC da ta cire Zakari domin ganin anyi zabe na gaskiya.

KU KARANTA KUMA: Ba za mu sake kuskuren zabar PDP ba – Masu sauya sheka

Ameh yace kamar yadda ya saura kasa da kwanaki 45 ayi zabe, hukumar za tafi daraja idan ta guji duk wasu rigingimu kamar wannan, inda yace ya amsa kira sama da 26 daga shugabannin jam’iyyu.

Yace Zakari wacce ta kasance kwamishina ta cancanci wannan matsayi sosai kasancewar ta taba aiki a matsayin mukaddashin shugabar INEC a baya, amma maganar da ake yi a yanzu na gudun zargi ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel