Yanzu yanzu: Kwastam ta damke motar Dangote dauke da haramtacciyar shinkafa

Yanzu yanzu: Kwastam ta damke motar Dangote dauke da haramtacciyar shinkafa

- Hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam), a jihar Adamawa, ta samu nasarar cafke wata babbar motar Dangote, makare da buhunan shinkafa 150

- Rundunarmu ta samu nasarar cafke shinkafar ne da aka shigo da ita ba bisa ka'ida ba, a kan hanyar Mayo zuwa Belwa, jihar Adamawa

- Hukumar ta samu nasarar tara akalla N168,294,227.83 daga watan Janairu zuwa watan Disamba, ba kamar yadda ta tara N186,113,181.28 a shekarar 2017 ba

Labarin da Legit.ng ke samu daga jaridar SaharaReporters, na nuni da cewa, Hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam), a jihar Adamawa, ta samu nasarar cafke wata babbar motar Dangote, makare da buhunan shinkafa 150, da aka shigo da su ta barauniyar hanya.

Kamardeen Olumoh, kwanturan hukumar kwastam, reshen Adamawa/Taraba, ya sanar da hakan, a lokacin da yake gabatar da motar gaban manema labarai a garin Yola, a ranar Juma'a.

"Rundunarmu ta samu nasarar cafke wata motar Dangote mai dauke da buhuna 150 na shinkafar kasar waje, da aka shigo da ita ba bisa ka'ida ba, a kan hanyar Mayo zuwa Belwa, a ranar karshe ta shekarar data gabata," a cewarsa.

"Direban ya samu damar arcewa, amma muna da tabbacin cewa, kasancewar Dangote dan kasa nagari, zai gano direban tare da mikashi ga hukuma don yanke masa hukuncin da hukuma ta tanadar a gareshi."

KARANTA WANNAN: Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta kori jami'inta da ya kashe wani dalibin jami'a

Yanzu yanzu: Kwastam ta damke motar Dangote dauke da haramtacciyar shinkafa

Yanzu yanzu: Kwastam ta damke motar Dangote dauke da haramtacciyar shinkafa
Source: Depositphotos

Kwanturola Olumoh ya kara da cewa, sauran kayan da rundunar ta cafke, sun hada da shinkafar, kayan gwamnjo da kuma kayan da aka hadasu daga man-fetur, wadanda ya kamata a biyawa sama da N69m idan ahr za a shigo da su.

Da yake bayar da bayani kan kayayyakin da hukumar ta samu nasarar cafkewa a shekarar data gabata, ya ce: "Hukumar ta samu nasarar cafke kaya har sau 61, wadanda kusan shinkafa 'yar kasar waje ne, da ta kai kimanin buhu 1,740.

Haka zalikja, an cafke motocin da aka yi amfani da su, da kayan gwanjo, da kuma litar man fetur 21,270, da kudin fansarsu yakai N59,781,006.81.

"A halin yanzu, akwai mutane 3 da ake tuhumarsu, kan sa hannu a fasa kwabrin kayan da aka haramta shigowa da su kasar," a cewarsa.

Haka zalika, Olumoh ya jaddada cewa kudin shiga da hukumar ta tara a cikin shekarar 2018 ya gaza yadda ake so, wanda ya alakanta hakan da matsalar tsaro da ambaliyar ruwa da ta shafi jihohin.

"Hukumar ta samu nasarar tara akalla N168,294,227.83 daga watan Janairu zuwa watan Disamba, ba kamar yadda ta tara N186,113,181.28 a shekarar 2017 ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel