Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago na ganawa a Abuja kan albashi

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago na ganawa a Abuja kan albashi

- Gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar kwadago na cikin ganawa a yanzu haka

- Suna tattaunawa ne akan lamarin mafi karancin albashi

- Daga cikin wadanda suka halarci ganawar sun hada da Ministan kwadago da diban ma’aikata, Ministar kudi, Ministan tsare-tsare na kasa

Gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar kwadago na cikin ganawa a yanzu haka a ma’aikatar kwadago da daukar aiki da ke Abuja akan mafi karancin albashi tare da kudirin samun mafita akan rigimar da ke tattare da sabon albashin na N30,000.

An kira taron ne domin bayar da karin bayani kan kokarin gwamnatin taraya na mika dokar sabon albashi ga majalisar dokokin kasa kamar yadda kungiyar NLC ta bukata, da kuma hanyar dakatar da zanga-zangar gama gari da kungiyoyin ke yi.

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago na ganawa a Abuja kan albashi

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago na ganawa a Abuja kan albashi
Source: Depositphotos

Daga cikin wadanda suka halarci ganawar sun hada da Ministan kwadago da diban ma’aikata, Dr Chris Ngige, Ministar kudi, Zainab Ahmed da Ministan tsare-tsare na kasa,Udoma Udo Udoma.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyyar PDP ta samu gagarumin karuwa a jihar Gombe

Tawagar da ke wakiltan kungiyar kwadagon sun hada da shugaban NLC, Ayuba Wabba, babban sakataren NLC, Peter Ozo-Eson, da shugaban TUC, Kaigama Bobboi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel