Sabuwar gidauniyar da zata kula da iyalan Sojin da aka kashe ta fara aiki

Sabuwar gidauniyar da zata kula da iyalan Sojin da aka kashe ta fara aiki

- An kaddamar da gidauniyar tallafi don tsofaffin sojoji da kuma iyalan wadanda suka rasa ransu

- Ma'aikatan gwamnati, shuwagabanni da yan kasuwa ne suka tallafa

- Anyi hakan ne don iyalan su suma su zauna cikin walwala

Sabuwar gidauniyar da zata kula da iyalan Sojin da aka kashe ta fara aiki

Sabuwar gidauniyar da zata kula da iyalan Sojin da aka kashe ta fara aiki
Source: Facebook

Kungiyar tsofaffin sojoji a ranar alhamis ta samu Naira miliyan 13.7 a matsayin kyautar ranar tunawa da sojoji a gidauniyar tallafi da aka bude don tsofaffin sojoji da kuma iyalan sojojin da suka rasa rayukan su.

Wakilinmu ya lura cewa mafi yawan kyautar da suka samu na Naira miliyan 3 ne da Naira miliyan 2 daga gwamnatin jihar sokoto da kuma shugaban masu kaddamar da gidauniyar, Sahabi Bodinga.

Kamfanin siminti na arewacin Najeriya, CCNN, ya bada kyautar Naira miliyan 1, ma'aikatan gwamnati na jihar sokoto sun hada Naira miliyan 3 da sauran masu mukamin siyasa a jihar sun bada Naira miliyan 1.

Haka kuma cibiyoyin tsaro na jihar sun hada Naira 500,000 ta hannun kwamishinan yan sandar jihar, Murtala Mani.

Mukaddashin shugaban alkalai, Mai shari'a Sa'idu Sifawa ya bada kyautar Naira 600,000 a madadin ma'aikatar shari'a ta jihar Sokoto, majalisar jihar ta bada Naira 300,000, jami'ar Usmanu Danfodio ta bada Naira 200,000 sai kuma asibitin koyarwa na jami'ar Usmanu Danfodio ya bada 100,000.

Masarautar Sokoto ma ba a barta a baya ba da wasu yan kasuwa.

Gwamna Aminu Tambuwal ya hori mutane da kungiyoyi da su tallafa domin walwalar iyalan sojojin da suka rasa rayukan su da wadanda suka yi ritaya.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Bashir Garba shine ya wakilci gwamnan. Yace kyautukan an bada su ne don tallafawa iyalan sojojin da suka rasa rayukan su wajen kare kasar mu.

DUBA WANNAN: Kalandar Najeriya a 2019: Ranekun da kuke da hutu tun daga wannan mako har Disamba

"Zamu cigaba da tallafawa musu da iyalan sojojin da suka rasa rayukan su wajen kawo zaman lafiya a kasar nan," Mista Tambuwal yace.

Aliyu Danchadi, shugaban kungiyar tsofafin sojojin yace an ware ranar tunawa da sojojin ne saboda wadanda suka rasa rayukan su wajen kare kasar nan don hadin kai da daidaituwar kasar nan.

Mista Danchadi ya jinjinawa gwamnatin jihar da kuma mutanen da suka tallafawa iyalan sadaukan kuma yana kara kira don kara tallafawa garesu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel