Amina Zakari ba jinin shugaba Buhari bace – Aliyu Abdullahi

Amina Zakari ba jinin shugaba Buhari bace – Aliyu Abdullahi

- Aliyu Abdullahi ya yi watsi da ikirarin jam’iyyar PDP na cewa Amina Zakari yar’uwar Muhammadu Buhari ce ta jini

- Abdullahi yace Buhari dan Daura ne a jihar Katsina yayinda Amina kuma ta kasance yar Jihar Jigawa

- A ranar Alhamis ne INEC ta nada Amina a matsayin shugabar kwamitin sanar da sakamakon zabe

Aliyu Abdullahi ya yi watsi da ikirarin jam’iyyar People Democratic Party (PDP) na cewa Amina Zakari yar’uwar Muhammadu Buhari ce ta jini, cewa shugaban kasar dan Daura ne a jihar Katsina yayinda Amina kuma ta kasance yar Jihar Jigawa.

Abdullahi, matamakin daraktan labaran kungiyar kamfen din Buhari, wanda ya kasance bako a shirin Sunrise Daily ya yi korafin cewa PDP na ba yan Najeriya bayanan karya.

Amina Zakari ba jinin shugaba Buhari bace – Aliyu Abdullahi

Amina Zakari ba jinin shugaba Buhari bace – Aliyu Abdullahi
Source: Twitter

Ya ci gaba da cewa kokawar da PDP ke yi akan nada Amina bai da wani karfi musamman saboda an taba nada ta a matsayin kwamishinar hukumar INEC a gwnain Goodluck Jonathan tun a shekarar 2011.

KU KARANTA KUMA: Ba za mu sake kuskuren zabar PDP ba – Masu sauya sheka

Ya kuma kara da cewa a ganinsa matsayin da aka ba Amina ko kadan baya da nasaba da sanar da sakamakon zabe, cewa ya fi kama da matsayin mai kula da daidaituwar komai yadda ya kamata.

Aliyu yace abunda ya kamata PDP ta mayar da hankali wajen ganewa shine “hukuma ce mai zaman kanta da bata bukatar wani daga waje ya zo ya shirya mata yadda za ta gudarda aikinta."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel