Ta'addanci ya salwantar da rayukan Mutane 5,113 cikin watanni 11 a bara

Ta'addanci ya salwantar da rayukan Mutane 5,113 cikin watanni 11 a bara

Hakika Hausawa na cewa wanda ya tuna bara bai ji dadin bana ba, hakan ta ke kuwa a kasar nan ta Najeriya sakamakon yadda ta'addanci a sanadiyar rashin tsaro ya salwantar da rayukan dubunnan Mutane cikin shekarar 2018 da ta gabata.

Binciken manema labarai na jaridar Vanguard ya tabbatar da cewa, akwai adadin rayukan Mutane 5,113 da suka salwanta a sakamakon aukuwar mummunar ta'ada daban-daban a tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba na shekarar da ta gabata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan adadi na rayukan da suka salwanta ya takaita ne kadai kan rahotannin da aka bayyana a bara domin kuwa ta'addanci ya salwantar da rayukan mutane da dama ba tare bayyana rahotannin su ba.

Ko shakka ba bu adadin rayukan Mutane da suka riga mu gidan gaskiya sun salwanta musamman a sanadiyar rikita-rikita ta kungiyoyi, arangama tsakanin makiya da manoma, tayar da kayar baya na Boko Haram, tarzoma ta kungiyoyin asiri da kuma fashi da makami.

Ta'addanci ya salwantar da rayukan Mutane 5,113 cikin watanni 11 a bara

Ta'addanci ya salwantar da rayukan Mutane 5,113 cikin watanni 11 a bara
Source: Depositphotos

Wannan kididiga ta adadin rayuka da suka salwantar ba ta hadar da wanda azal ta garkuwa da mutane ta afka masu ba. Kazalika binciken bai hadar da rayukan da suka salwanta ba a sanadiyar barkewar annoba ta cututtuka, hatsari, ambaliyar ruwa, zazzabin Lassa da makamantan su.

Kididdigar ta bayyana cewa, yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da tayar da kayar na kungiyar ta'adda ta Boko Haram ya yi kamari, ya sanya adadin rayukan da suka salwanta ya yiwa na sauran yankunan Najeriya fintinkau fiye da kima.

Ta'addanci ya salwantar da rayukan Mutane 2,408 a Arewa maso Gabashin Najeriya, yayin da rayukan Mutane 1,835 suka salwanta a Arewa ta Tsakiya da kuma rayukan Mutane 1,075 da suka salwanta a Arewa maso Yamma.

Yankunan Najeriya da a iya zaman lafiya ya wadata daidai gwargwado sun hadar da Kudu maso Gabashin Najeriya inda adadin rayuka 112 kacal suka salwanta. Yankin Kudu maso Yamma na Najeriya ya yi asarar rayukan Mutane 224 yayin da kudancin Kudu ya yi asarar rayukan Mutane 462 cikin watanni 11 na shekarar bara.

KARANTA KUMA: Akwai kitimurmurar da Buhari ya kulla da gwamna Yari na jihar Zamfara - Atiku

Ga Dalla-Dalla dangane da adadin rayukan da suka salwanta cikin kowace jiha ta Najeriya a sakamakon tarzoma ta ta'addanci:

Borno (1,582), Filato (684), Benuwe (640), Kaduna (458), Zamfara (408), Adamawa (407), Taraba (315), Nasarawa (223), Edo (150), Kogi (121), Legas (86), Ribas (85), Delta (79), Kuros Riba (78), Yobe (76), Abuja (70).

Sauran jihohin sun hadar da; Kwara (62), Sakkwato (56), Katsina (51), Ondo (51), Anambra (40), Ebonyi (36), Bayelsa (38), Kano (33), Neja (35), Jigawa (30), Bauchi (18), Abia (17), Ekiti (14), Oyo (12), Enugu (10), Gombe (10), Imo (9) da kuma Osun (4).

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel