An kai kayan agaji jihar Zamfara bayan sabbin kashe-kashen da aka yi

An kai kayan agaji jihar Zamfara bayan sabbin kashe-kashen da aka yi

- NEMA ta mika gudummawar abubuwan amfani ga mutanen Tsafe dake jihar Zamfara

- Da yake magana bayan karbar kayan Abubakar Yusuf yace kayan sun fito ne daga gwamnatin tarayya

- Sakataren SEMA Sanusi Kwatarkwashi ya nuna jindadin sa bisa ga wannan abu da NEMA tayi

An kai kayan agaji jihar Zamfara bayan sabbin kashe-kashen da aka yi

An kai kayan agaji jihar Zamfara bayan sabbin kashe-kashen da aka yi
Source: Facebook

Hukumar nan ta bada taimakon gaggawa (NEMA) ta mika kayan amfanin yau da kullum ga al'ummar Tsafe dake jihar Zamfara.

Da yake magana bayan karbar wadannan kaya a ranar Alhamis shugaban NEMA yankin jihar Sokoto Abubakar Yusuf ya bayyana cewa wadannan kaya sun fito ne daga gwamnatin tarayya dan karfafawa wadanda abun ya shafa gwiwa.

DUBA WANNAN: Ko da taimakonku ko babu shugaba Buhari ya zarce ya gama, Ngige ya gaya wa kabilarsa ta Igbo

Mr Yusuf yace kayan da aka kai musu sun hada da buhunhunan shinkafa 250,Gero 250,Masara 250,buhun Omo 100,katan din sabulu 100,tabarmi 300 da kuma cokula 300.

Ragowar kayan sun hada dz bokitan ruwa,gidan sauro,jarkokin man gyada,kofuna da kuma katifu.

Ya kara da cewa akwai karin wasu kayan da hukumar zata kawo.

Da yake nuna farin cikin sa sakataren hukumar na jihar SEMA Sanusi Kwatarkwashi ya mika godiyar sa ga NEMA bisa ga wannan abu da tayi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel