Ba za mu sake kuskuren zabar PDP ba – Masu sauya sheka

Ba za mu sake kuskuren zabar PDP ba – Masu sauya sheka

Mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da suka sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC) a kauyen Tika da ke yankin Kuje, sun shugabansu, Abdullahi D. Galadima, cewa sun yi danasanin kuskuren da suka yi a zabar jam’iyyar adawa a zaben da ya gabata.

Wani tsohon shugaban PDP a Tika, Mista Ayi Gyiayegbe, ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci mambobin PDP 1,245 zuwa APC a jiya, a yankin cewa ba za su maimaita irin wannan kuskuren ba a zaben Fabrairu da Maris.

Yace hukuncin da ya yanke na komawa APC daaga PDP saboda tarin kokarin da gwamnatin Galadima tayi ne a Kuje, inda ya bayyana cewa shugaban ya taimaki mutane da dama a yankin duk da banbancin siyasa.

Ba za mu sake kuskuren zabar PDP ba – Masu sauya sheka

Ba za mu sake kuskuren zabar PDP ba – Masu sauya sheka
Source: Depositphotos

Yace zai tabbatar da cewar mambobin PDP, musamman mata da matasa da suka sauya sheka zuwa APC sun jajirce wajen ganin nasarar jam’iyyar a yanzu tun daga matakin shugaban kasa har zuwa kansila.

KU KARANTA KUMA: Mayun Najeriya sun fada ma Atiku yadda zai iya kayar da Buhari a 2019

Shugaban yankin Alhaji Abdullahi D. Galadima wanda ya tarbi ,masu sauya shekar ya yaba masu da suka gane manufar APC da gwamnatinsa.

Ya ba masu sauya shekar tabbacin cewa a matsayinsa na jigon APC za su yi aiki tare da su akan kowace shawara da jam’iyyar za ta yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel