Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa ba za mu sauke Amina Zakari daga matsayinta ba - INEC

Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa ba za mu sauke Amina Zakari daga matsayinta ba - INEC

- Hukumar ta kuma karyata ikirarin cewa ta hanyar jagorantar kwamitin, Zakari za ta kasance cikin hada sakamako

- Wasu yan Najeriya ciki harda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun ki amincewa da nadin Amina da INEC ta yi

- INEC tace aikinta shine tabbatar da cewar komai ya hadu amma ba wai ita ce za ta sanar da sakamakon zaben ba

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tace ba ta shirin tsige Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin sanar da sakamakon zabe ba.

Hukumar ta kuma karyata ikirarin cewa ta hanyar jagorantar kwamitin, Zakari za ta kasance cikin hada sakamako.

INEC ta sanar da nadin Zakari a matsayin shugabar kwamitin a ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu lokacin da ta kaddamar da kwamitocin zaben.

Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa ba za mu sauke Amina Zakari daga matsayinta ba - INEC

Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa ba za mu sauke Amina Zakari daga matsayinta ba - INEC
Source: Twitter

Amma wasu yan Najeriya ciki harda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun ki amincewa da hukuncin.

PDP tayi ikirarin cewa Amina Zakari, wanda tana cikin manyan jami’an hukumar INEC, diya ce a wurin shugaban kasa Buhari. A dalilin haka ne jam’iyyar adawar ta ke ganin zai yi wahala jami’ar zaben ta bari Buhari ya sha kasa a 2019.

KU KARANTA KUMA: Mayun Najeriya sun fada ma Atiku yadda zai iya kayar da Buhari a 2019

Don haka da yake magana a wani shirin Channels TV a ranar Juma’a, Oluwole Osaze-Uzzi, daraktan INEC na ilimantar da masu zabe da labarai, yace kwamitin Zakari zai kula ne da lamuran zaben.

Yace aikinta shine tabbatar da cewar komai ya hadu amma ba wai ita ce za ta sanar da sakamakon zaben ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel