Bankin Duniya zai raba Naira Biliyan 50 ga ‘Yan gudun hijira a Najeriya

Bankin Duniya zai raba Naira Biliyan 50 ga ‘Yan gudun hijira a Najeriya

Mun samu labari daga Jaridar Leadership cewa babban bankin Duniya na daf da shirin rabawa Bayin Allah da ke gudun hijira a Yankin Arewa maso gabashin kasar nan kudi domin su kama kananan sana’a.

Bankin Duniya zai raba Naira Biliyan 50 ga ‘Yan gudun hijira a Najeriya

Wasu ‘Yan gudun hijira a Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
Source: UGC

Babban bankin na Duniya zai rabawa mutane sama da 200, 000 da ke sansanin gudun hijira na IDP a jihar Borno kudi har Naira 200, 000 domin su samu jarin kama sana’a. Wannan yana cikin tsarin bankin na taimakawa Matasan yankin.

Wani jami’in babban bankin Duniyar kuma wanda ke kula da wannan tsari da zai tallafawa Matasan da ke sansanin IDP watau Zanna Hassan Boguma, shi ya bayyana wannan. Zanna Boguma ya bayyana wannan ne a makon nan.

KU KARANTA: Akwai lauje a cikin nadi game da kisan wani Soja inji Rahoton kungiyar Amurka

Za a rabawa matasan kudin ne lokaci-bayan-lokaci, inda yanzu za a soma da ba su N30, 000. Daga baya kuma za a kara masu N100, 000 sannan kuma N50, 000 da N20, 000 da zarar sun koma gidajen su da ‘yan ta’addan Boko Haram su ka fatattake su.

Bankin na Duniya yana da burin ganin wadanda ‘yan ta’adda su ka kora daga gidajen su, sun tashi da kafafun su. Wannan ya sa aka zabi matasa 264, 000 a Borno da ke cikin Yankin Arewa maso Gabashin kasar domin ganin an kawo masu dauki.

Wannan tallafi da za a bada zai taimaka wajen ganin mutane sun rungumi kanana sana’o’i wanda za su rike su. Zanna Hassan Boguma duk yayi wannan jawabi ne lokacin da ya gana da ‘yan gudun hijiran da su ka fake a Garin Muna a Jihar Borno.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel