Dalilin da yasa Buhari ya kaddamar da yakin neman zabensa a Akwa Ibom - Masari

Dalilin da yasa Buhari ya kaddamar da yakin neman zabensa a Akwa Ibom - Masari

- Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya ce ba kuskure bane Buhari ya zabi Uyo domin kaddamar da yakin neman zabensa na 2019

- Gwamna Masari ya ce jam'iyyar APC ta zabi jihar Akwa Ibom ne domin tana son ta gwada irin kwarjinin da Buhari ke da shi a yankin

- Masari ya ce al'umma cin cika filin motsa jiki na Uyo makil wadda hakan ya nuna mutanen yankin suna tare da Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya yi tsokaci a kan dalilin da yasa Shugaba Muhammadu Buhari ya kadamar da yakin neman zabensa a jihar Akwa Ibom da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.

A hirar da ya yi da Daily Trust, Gwamna Masari ya ce jam'iyyar APC ta zabi Uyo, da ke Akwa Ibom ne domin tana son ta gwada kwarjinin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ke da shi a yankin Kudu dubba da cewa ya fi samun kuri'u masu yawa a jihohin Arewa ne a zabukkan baya.

Dalilin da yasa Buhari ya kaddamar da yakin neman zabensa a Akwa Ibom

Dalilin da yasa Buhari ya kaddamar da yakin neman zabensa a Akwa Ibom
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC ta ce tana tausayin wani gwamnanta

"Idan kana son ka gwada kwarjinin ka, ka tafi yankin da baka da magoya baya sosai. Mutanen yankin Kudu maso Kudu daga wurare da yawa sun hallarci kaddamar da yakin zaben sun cika filin motsa jikin makil.

"Wadanda ke zargin Buhari ya dauki hayar mutane tabbas ba su san shi ba, Buhari bai taba yiwa kansa fosta ba ma ballanta ya dauki hayar mutane. Duk wani fostan Buhari da ka gani, wani ya dauki nauyin buga ta saboda yana cika wa mutane alkawurran da ya dauka," inji Masari.

"Haka muka koya daga shugabaninmu da suka shude. Mallam Aminu Kano bai tara akwatunnan kaya ba amma har zuwa karshen rayuwarsa, yana samun duk abinda ya ke so. Ba mu bukatan abubuwa masu yawa a rayuwa ila wurin kwanciya, asibiti domin marasa lafiya da abinci da zamu ci.

"Duk wanda ya ce Buhari karya ya ke ya nuna mana inda Buhari ya ajiye kudadensa saboda wasu sun kai matsayinsa kuma irin rayuwar da su kayi ya nuna cewa akwai alamun sun saci kudi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel