Akwai kitimurmurar da Buhari ya kulla da gwamna Yari na jihar Zamfara - Atiku

Akwai kitimurmurar da Buhari ya kulla da gwamna Yari na jihar Zamfara - Atiku

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya ce yana maraba da duk wani mataki na hankali da gwamnatin tarayya za ta dabbaka wajen kawo karshen salwantar rayukan al'umma a jihar Zamfara da kuma Katsina.

Atiku ya ke cewa, akwai babbar bukata da ta rataya a wuyan gwamnati domin kawo karshen tabargaza ta zubar jini gami a asarar rayuka da dukiyoyin al'umma a jihar Zamfara da kuma Katsina.

Sai dai ya ce shimfida dokar ta baci a jihohin biyu ba zai wani tasiri ba illa iyaka harzuka tarzoma ta rashin tsaro da jihohin ke fuskanta a halin yanzu.

Yayin martani dangane da kiran gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, na shimfida dokar ta baci a jihar sa, Atiku ya ce hakan ba zai kawo karshen matsalar ba wajen neman zaman lafiya na dindindin.

Akwai kitimurmurar da Buhari ya kulla da gwamna Yari na jihar Zamfara - Atiku

Akwai kitimurmurar da Buhari ya kulla da gwamna Yari na jihar Zamfara - Atiku
Source: Twitter

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne da sanadin babban hadimin sa na musamman kan hulda da manema labarai, Mista Phrank Shu'aibu, kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.

Turakin na Adamawa ya ke cewa, wannan kira wani yunkuri ne na kulla tuggu tsakanin gwamna Yari da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar sa ta APC, domin samun damar kwace jihar Zamfar a yayin babban zaben kasa da za a gudanar watan gobe.

Ko shakka ba bu kawowa yanzu ba bu gwanin takarar gwamna a jihar Zamfara karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, da a cewar Atiku neman shimfida dokar ta baci wata dabara ce ta jam'iyyar domin tsayar da dan takara a yayin kiciniyar samar da tsaro a jihar.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nemi kungiyar ASUU ta janye yajin aiki

Ya yi kira ga gwamna Yari a kan ya gaggauta yin murabus sakamakon gazawar sa ta bayar da kariya ga lafiya da kuma dukiyoyin al'ummar sa da ya sha alwashin tseratarwa yayin karbar akalar jagorancin jihar.

Ya kara da cewa, jam'iyyar PDP a tsaye ta ke kyam kuma ba za ta gushe ba wajen yunkurin ta da kuma fafutika ta ceto martabar kasar nan daga mulkin kama karya mai durkusar da duk wani ci gaba da habakar kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel