Shugaba Buhari ya nemi kungiyar ASUU ta janye yajin aiki

Shugaba Buhari ya nemi kungiyar ASUU ta janye yajin aiki

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar sa dangane da yajin aikin kungiyar ASUU da ke neman dagula ma sa lissafi

- Shugaba Buhari ya yi rarrashi ga kungiyar kan cewa gwamnatin sa na iyaka bakin kokarin ta

- Kungiyar Daliban Najeriya ta NANS ta ziyarci shugaba Buhari a fadar sa ta Villa da ke garin Abuja

A jiya Alhamis shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika kokon barar sa ga kungiyoyin kwadago da dama da ke fadin kasar nan a kan su sassauta fushin su da tayar da kayar baya domin gwamnatin sa ta samu damar mayar da hankalin ta wuri guda na habaka da inganta ci gaban kasa.

Shugaban kasa Buhari ya yi wannan furuci ne yayin ganawarsa da kungiyar Daliban Najeriya ta NANS, National Association of Nigerian Students, a fadar sa ta Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Shugaba Buhari ya nemi kungiyar ASUU ta janye yajin aiki

Shugaba Buhari ya nemi kungiyar ASUU ta janye yajin aiki
Source: UGC

Shugaba Buhari kai tsaye ya bayyana damuwarsa dangane da yajin aikin kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU, da cewar ya kamata ta nuna hali na kyautuwa ga kwazo da kuma bajintar gwamnatin sa yayin da ta ke fafutika da kuma yunkurin inganta ci gaban gine-gine a fadin kasar nan..

Ya ke cewa ko shakka ba bu, gwamnatin sa ta yi kwazon gaske gami da kyakkyawar bajinta ta inganta ci gaban gine-gine a dukkanin sassan kasar nan tsawon shekaru uku da rabi da ta shafe a bisa karagar mulki da jagoranci.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne da sanadin babban hadimin sa na mussaman kan hulda da manema labarai da kuma al'umma, Mista Femi Adesina.

Buhari ya kara da cewa, za ya nemi ganawa da kungiyar malamai ta ASUU domin rarrashi akan janye yajin aikin da ta afka cikin kasar nan tsawon watanni biyu da suka gabata.

KARANTA KUMA: Furucin nuna kiyayya na barazana da rashin zaman lafiya - Sarkin Zuru

Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar ASUU na ci gaba da tayar da kayar baya a sakamakon rashin cika alkawari daga bangaren gwamnatin tarayya na inganta jin dadin malamai da kuma dalibai ta fuskar habakar gine-gine da kuma kayan kararu na zamani a jami'o'in kasar nan.

A nasa jawaban, jagoran kungiyar daliban Najeriya ta NANS, Danielson Bamidele Akpan, ya yabawa kwazo da kuma bajintar gwamnatin shugaba Buhari musamman a bangaren yaki da ta'addanci a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel