Bakare ya yi magana game da zama shugaban kasar Najeriya na 16 (bidiyo)

Bakare ya yi magana game da zama shugaban kasar Najeriya na 16 (bidiyo)

- Fasto Tunde Bakare na cocin Latter Rain Assembly, yace ya fada ma shugaba Buhari cewa shi (Bakare) ne zai zamo shugaban kasar Najeriya na 16

- Ya ce ya sanar da shugaba Buhari game da shirinsa don kawai kada a yi masa mumunan fahimta

- Bakare ya ce yanzu haka yana gina wani ahli na siyasa daga fadin duniya, wanda zai yi amfani da shi akan kudirin siyasar sa anan gaba

Yayinda zaben 2019 ke ta gabatowa, babban limamin cocin Latter Rain Assembly, Fassto Tunde Bakare, yace ya fada ma shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa shi (Bakare) ne zai zamo shugaban kasar Najeriya na 16.

Malamin wanda yake mazaunin Lagas ya fadi hakan a wani hira da aka yi dashi a Calgary, kasar Canada, ya kara da cewa a yanzu haka yana gina wani ahli na siyasa daga fadin duniya, wanda zai yi amfani da shi akan kudirin siyasar sa anan gaba, jaridar TheCable ta ruwaito.

Bakare ya yi magana game da zama shugaban kasar Najeriya na 16 (bidiyo)

Bakare ya yi magana game da zama shugaban kasar Najeriya na 16 (bidiyo)
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa Bakare yace shugaba Buhari ne shugaban kasa na 15 sannan cewa shi (Bakare) ne zai zamo na 16.

A cewar Bakare,ya sanar da shugaba Buhari game da shirinsa don kawai kada a yi masa mumunan fahimta.

KU KARANTA KUMA: Aisha ta nuna alamun 4+4 don marawa tazarcen Buhari baya (hoto)

Ya kara da cewa: “Kuma na fada ma shugaban kasa saboda bana do ayi mani mumunan fahimta, saboda wadannan abubuwa ne da ke yawo duk a fadin duniya.

“Nace ya shugaba, Ina gina wani ahli na siyasa saboda kudirin takara na a nan gaba; kaine na 15, sannan ni zan zamo na 16.”

Kalli bidiyon a kasa:

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel