Ku kyale ni in yiwa mutane aiki - Buhari ya roki kungiyoyin dake yajin aiki

Ku kyale ni in yiwa mutane aiki - Buhari ya roki kungiyoyin dake yajin aiki

Shugaba Muhammadu Buhari ya koka kan yadda kungiyoyin da ke yajin aiki a Najeriya ba su la'akari da irin ayyukan da gwamnatinsa ke yiwa al'ummar kasar nan. Ya roki kungiyoyin su janye yajin aikin saboda gwamnatinsa ta mayar da hankali kan inganta ruyuwan 'yan Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya roki kungiyoyin da ke yajin aiki a Najeriya su rage korafe-korafen da su keyi domin bawa gwamnatinsa daman mayar da hankali a kan gyara kayayakin da suka lalace a kasar.

Punch ta ruwaito cewa shugaban kasar ya yi wannan kirar ne yayin ganawarsa da shugabanin kungiyar daliban Najeriya na kasa (NANS) a ranar Alhamis a fadar Aso Villa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Buhari ya ambaci kungiyar malaman jami'o'i na kasa ASUU inda ya bukaci malaman suyi la'akari da irin na mijin kokarin da gwamnatinsa keyi a bangaren gyare-gyaren abubuwan da suka lalace a Najeriya.

Ku kyale ni in yiwa mutane aiki - Buhari ya roki kungiyoyin dake yajin aiki

Ku kyale ni in yiwa mutane aiki - Buhari ya roki kungiyoyin dake yajin aiki
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An nadi faifan bidiyon wani malamin islamiyya yana lalata dalibarsa mai shekaru 5

"A cikin shekaru uku da rabi, mun samun gagarumin nasara a bangaren inganta rayuwar al'umma idan aka kwatanta da abinda muka samu yayin da muka karba mulki.

"A dukkan bangarorin Najeriya, muna kokarin gyara layukkan dogo, muna gyara wutan lantarki ta hanyar amfani da iskar gas da hasken ranar.

"Idan ku kayi la'akari da ayyukan da mu kayi cikin shekaru uku da rabi, ba za kuyi da na sanin zaben gwamnatin mu ba," a cewar Buhari a cikin wata sanarwa da hadiminsa Mr Femi Adesina ya fitar.

Buhari ya kara da cewa zai tattauna da ASUU domin su janye yajin aikin da su keyi saboda kada su kawo wa dalibai cikas wurin kammala karatunsu na digiri a kan lokaci.

Shugaban kasar ya ce kowa ya san cewa babu kudi a Najeriya kamar yadda ya nuna cikin kasafin kudin shekarar 2019 da ya gabatar.

A jawabinsa, shugaban NANS, Danielson Bamidele -Akpan ya yabawa shugaba Muhammadu Buhari kan kokarinsa na magance ta'addanci a yankin Arewa maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel