Aisha ta nuna alamun 4+4 don marawa tazarcen Buhari baya (hoto)

Aisha ta nuna alamun 4+4 don marawa tazarcen Buhari baya (hoto)

- Uwargidan shugaban kasa Buhari, Aisha ta yi shiri tsaf domin marawa maigidanta baya a 2019

- Ta yiwa yatsun hannayenta lalle domin baje kolin alamar 4+4

- Tuni dai aka kaddamar da tawagar kamfen din shugaban kasar wanda Aisha ke jagoranta

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta fara yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kamfen din mataki na gaba wato ‘Next level’ ta hanyar yiwa yatsun hannayenta lalle domin baje kolin alamar 4+4.

Legit.ng ta tattaro cewa ta yi nuni ga alamun 4+4 din ne ta hanyar ‘daga da yatsun hannayenta hudu daga bangaren dama da hagu. Wannan alama na nuna cewa tana sake nema wa shugaba Buhari wasu shekaru hudu anan gaba bayan ya kammala wannan zangon.

Uwargidan shugaban kasar ta sha alwashin marawa mijinta baya a kudirinsa na neman yin tazarce yayinda aka kaddamar da tawagar kamfen dinta na mata da matasa a ranar Alhamis, ga watan Janairu a Abuja.

Aisha ta nuna alamun 4+4 don marawa tazarcen Buhari baya (hoto)

Aisha ta nuna alamun 4+4 don marawa tazarcen Buhari baya (hoto)
Source: UGC

A wani yunkuri na daban, uwargidan Buhari ta sanar da cewa tawagar kamfen din za su yi aiki tare da kungyar kamfen din shugaban kasar.

An bayyana tawagar kamfen din a matsayin tawagar kamfen na mata da matasa don zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Ku fara shiga sako-sako ku na kamfe – Buhari ya fadawa ‘Yan APC

Anyi bikin kaddamar da kungiyar ne a anquet Hall da kee fadar shugaban kasa a Abuja da misalin karfe 3 da yan mintuna.

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ce ke jagorantar kungiyar, yayinda uwargidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo ce mataimakiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel