Abin da ya sa Yarbawa za su zabi Shugaba Buhari a 2019 – Olusola Oke

Abin da ya sa Yarbawa za su zabi Shugaba Buhari a 2019 – Olusola Oke

Daya daga cikin jiga-jigan yakin neman zaben Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo a kudancin Najeriya, Olusola Oke, ya bayyana cewa mutanen kasar Yarbawa za su marawa APC baya ne a 2019.

Abin da ya sa Yarbawa za su zabi Shugaba Buhari a 2019 – Olusola Oke

Idan har Atiku yayyi nasara, mulki zai bar Kasar Yarbawa inji Oke
Source: Facebook

Olusola Oke, wanda shi ne mataimakin Darektan yakin neman zaben Buhari a kudu maso yammacin Najeriya ya tabbatar da cewa idan APC ta cigaba da mulki, mutanen kasar Yarbawa za su amfana, akasarin idan PDP tayi nasara.

Oke wanda ya taba neman gwamnan jihar Ondo a karkashin jam’iyyar AD, ya fadawa manema labarai a Garin Ibadan jiya cewa za a cigaba da damawa da Yarbawa a kasar muddin shugaba Buhari da Osinbajo su ka zarce kan karagar mulki.

Oke ya gargadi mutanen kudu ta yamma cewa idan har PDP ta lashe zabe, mulki zai bar kasar Yarbawa. Tsohon ‘Dan takarar gwaman yace idan har APC ta sha kashi a zaben da za ayi, ayyuka da dama za su tsaya cak a Yankin Yarbawa.

KU KARANTA: Buhari ya fadawa Matasan APC su fara shiga sako-sako su na kamfe

Cif Olusola Oke dai ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta fara shimfidar gyara kasar ne, inda yace shiyasa wasu ba su ganin irin kokarin da ake yi a halin yanzu. Oke yace Buhari yana dasa shimfida ne kafin a cigaba da dora gini a Najeriya.

‘Dan siyasar ya gargadi jama’a da su yi bakin kokari wajen ganin wani dabam bai samu darewa kan mulkin kasar ba, domin a cewar sa, idan har aka sake zaben wani shugaban kasa a 2019, za a rusa ginin da shugaba Muhammadu Buhari ya fara yi.

Tsohon ‘Dan jam’iyyar adawa ta AD ya nuna cewa babu shakka Buhari ne zai yi nasara a zaben da za ayi a watan gobe tun da har APC ta iya lashe zabe a 2015 lokacin da ba ta da adadin Gwamnonin da ke da su kamar yanzu a Kudu maso yammacin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel