Jiragen yakin Sojojin Najeriya sun yi ma yan bindiga ruwan azaba a Zamfara

Jiragen yakin Sojojin Najeriya sun yi ma yan bindiga ruwan azaba a Zamfara

Rundunar dakarun Sojan sama ta sanar da cewar dakarunta da ake aikin Operation Diran Mikiya ta samu nasarar halaka yan bindiga da dama a sansaninsu dake kusa da dutsen Doumbourou, a jahar Zamfara, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.com ta ruwaito daraktan watsa labaru na rundunar, Iya komodo Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 3 ga watan Janairu, inda yace Sojojin sun kasha yan bindigan ne a ranar Laraba da taimakon jiragen yaki da suka dinga sakar musu wuta.

KU KARANTA: Mutuwar Sojoji a jirgin sama: Buratai ya kai ma babban hafsan Sojan sama ziyarar ta’aziyya

Jiragen yakin Sojojin Najeriya sun yi ma yan bindiga ruwan azaba a Zamfara

Jiragen yakin Sojojin Najeriya
Source: Facebook

A cewar kaakakin rundunar, “A ranar Laraba 2 ga watan Janairu ne rundunar Sojan sama ta samu bayanan sirri game da taruwar yan bindiga a kusa da dutsen Doumbourou, daga nan sai rundunar ta aika da jiragen yaki don su tabbatar da gaskiyar lamarin ko akasin haka.

“Shawagin da jiragenmu suka yi a sararin samaniyar yankin sun gano dandazon yan bindiga dauke da muggan makamai inda suke taruwa akai akai a gindin dutsen Doumbourou kafin su fita wajen aikata miyagun ayyukansu.

“Bayan samun wannan bayanai ne rundunar Sojan sama ta tura wasu manyan jiragen yaki guda biyu don fafatawa da yan bindigan, a hari na farko da jiragen suka kai sun tarwatsa sansanin yan bindigan tare da kasha wasu daga cikin yan bindigan.

“Hari na biyu kuwa ya baiwa Sojoji amfani da jiragen wajen karkashe yan bindigan yayin da suka firfito daga wuraren da suke fakewa, hakan yasa Sojoji suka yi musu kisan kiyashi, daga cikin wadanda aka kasha har da shugaban yan bindigan.” Inji Daramola.

Daga karshe kaakaki Daramola yace zasu cigaba da aiki tukuru tare da sauran rundunonin Soji, da ma hukumomin tsaro daban daban don cigaba da kai ma yan bindiga hare hare a duk inda suke, tare da dawo da zaman lafiya jahar Zamfara da keyawe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel