An zargi Shugaban kasa Buhari da saba yarjeniyar da aka shiga na zaben 2019

An zargi Shugaban kasa Buhari da saba yarjeniyar da aka shiga na zaben 2019

Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa baki daya, Timi Frank, yayi kira ga kwamitin da ke kokarin ganin an yi zaben Najeriya cikin lumuna, da ta takawa shugaba Buhari burki.

An zargi Shugaban kasa Buhari da saba yarjeniyar da aka shiga na zaben 2019

Timi Frank yace APC na shirin murde zaben 2019
Source: Depositphotos

Timi Frank, ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da sabawa yarjejeniyar da ya sa hannu na zaman lafiya a zaben 2019. Frank yayi wannan jawabi ne a Ranar Alhamis dinnan inda yace shugaban kasar yayi watsi da yarjejeniyar da aka yi.

Kwanakin baya jam’iyyun Najeriya su ka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar lumuna inda su kayi alkawari wanzar zaman lafiya a zabe mai zuwa. Timi Frank, wanda yanzu ya koma jam’iyyar adawa, yace Buhari yayi watsi da wannan shiri.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya fadawa Magoya bayan APC abin da za su yi a 2019

A jawabin na Timi Frank, ya zargi gwamnatin APC mai-ci da kokarin hana ‘yan adawa sakat a kasar. A cewar sa, hakan ya sabawa alkawarin da aka yi a baya. Frank yace akwai rashin adalci da danniya a tafiyar shugaba Muhammadu Buhari.

Kwamared Timi Frank ya zargi gwamnatin Buhari da amfani da dukiyar gwamnati wajen yi wa kan sa kamfe. Sannan kuma Frank yana zargin cewa ana amfani da jami’an tsaro wajen muzgunawa ‘yan adawa da kokarin ganin bayan su.

Timi Frank yana ganin cewa APC na kokarin murde zaben kasar kamar yadda yace aka yi a jihar Osun. Sai dai a cewar tsohon jami’in na APC, jama’an Najeriya a shirye su ke wajen ganin sun yi waje da gwamnatin APC a zaben da za ayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel