PDP ta fara banbami bayan INEC ta ba Amina Zakari sabon mukami

PDP ta fara banbami bayan INEC ta ba Amina Zakari sabon mukami

Jam’iyyar hamayya ta Najeriya watau PDP tayi tir da nada Amina Zakari da aka yi a matsayin shugaban kwamitin da zai sanar da sakamakon zabe tare da kuma ba hukumar shawara a kan zaben 2019.

PDP ta fara banbami bayan INEC ta ba Amina Zakari sabon mukami

Jam'iyyar PDP ta fadawa INEC ta sauke Amina Zakari daga sabon matsayin ta
Source: Twitter

PDP ta bayyana cewa ba za ta amince da wannan mukami ba, ganin cewa Hajiya Zakari, ‘Yar uwa ce a wurin shugaban kasa Muhammadu Buhari. PDP ta fitar da wannan jawabi ne ta bakin wani babban jami’in ta a jiya Alhamis.

Darektan yada labarai na PDP, Kola Ologbondiyan, ya bayyanawa manema labarai cewa akwai makarkashiya a wannan shiri da hukumar zabe na kasa watau INEC tayi. Jam’iyyar ta PDP ta na ganin ana yunkurin yin murdiya.

KU KARANTA: 2019: PDP tana sambatun da ta saba ne inji Shugaban INEC

Jam’iyyar adawar kasar ta kuma yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya nemi ‘Yar uwar ta sa ta ajiye wannan matsayi da aka daura mata, idan har da gaske gwamnatin sa na da niyyar ganin an yi zabe na gaskiya a shekarar nan.

PDP tayi ikirarin cewa Amina Zakari, wanda tana cikin manyan jami’an hukumar INEC, diya ce a wurin shugaban kasa Buhari. A dalilin haka ne jam’iyyar adawar ta ke ganin zai yi wahala jami’ar zaben ta bari Buhari ya sha kasa a 2019.

Mista Ologbondiyan yace nada Zakari a matsayin wanda za ta sanar da sakamakon zaben na 2019, ya nuna irin shirin sai-dai-a-mutu da gwamnatin APC ta ke yi wa zaben kasar. PDP tace Zakari za ta murde zabe domin APC tayi nasara.

KU KARANTA: Hukumar INEC ta bada muhimmiyar sanarwa a kan zaben 2019

A cewar Darektan na PDP, an yi amfani da Zakari wajen murde zaben Osun inda APC tayi nasara bayan PDP ta zo daf da lashe zaben. PDP ta nemi manyan kungiyoyin kasashen waje su kawo dauki domin hana yin murdiya a zaben kasar.

PDP ta kuma zargi Zakari da taimakawa Buhari a zaben 2015 ta hanyar yi wa kananan yara rajista domin su zabi APC. A takaice dai jam’iyyar ta nemi shugaban INEC ya janye wannan mukami da ya ba Hajiya Amina Zakari cikin gaggawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel