An sake kwatawa: Gungun yan bindiga sun halaka wani babban jami’in karamar hukuma

An sake kwatawa: Gungun yan bindiga sun halaka wani babban jami’in karamar hukuma

Rayuwa da wahala, yayin da da ake fama da matsalar ayyukan yan bindiga a jahar Zamfara, haka zalika ba’a kamala yaki da yayan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ba, sai gashi matsalar ayyukan yan bindiga na bullowa daga sassan yankin kudancin Najeriya.

Anan ma wasu gungun yan bindiga ne suka halaka ma’ikacin karamar hukumar Emure ta jahar Ekiti, Mista Abayomi Ajayi, wanda shine babban jami’I a ofishin kididdigar kudi na karamar hukumar, inji rahoton jaridar Daily Trust.

KU KARANTA; Matsalar Boko Haram: Ministan tsaro ya dira garin Maiduguri don gane ma idanunsa

Majiyar Legit.com ta ruwaito yan bindigan sun kashe Ajayi ne a wani harin kwantan bauna da suka yi masa a daren Laraba 2 ga watan Janairu da misalin karfe 8 na dare, yayin da yake komawa gida daga aiki.

Wannan lamari dai ya faru ne akan hanyar Ikere zuwa Ise, inda baya da kashe Mista Ajayi, yan bindigan sun yi awon gaba da abokan tafiyarsa guda biyu, wadanda dukansu ma’aikatan karamar hukumar ne.

Mutane biyu da yan bindigan suka yi garkuwa dasu sun hada da jami’in kula da ayyukan hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko, Dakta Fashin da kuma jami’in tafiyar da mulki, Fasto Onaade, kuma zuwa yanzu barayin sun nemi a biyasu naira miliyan goma ga duk mutum guda.

Itama rundunar Yansandan jahar Ekiti ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kaakakinta Caleb Ikechukwu, wanda ya bayyana cewa tuni kwamishinan Yansandan jahar ya bada umarnin fara binciken lamarin ganga ganga.

A wani labarin kuma rundunar Yansandan jahar Benuwe ta bayyana cewa ta kama wani matashi mai karancin shekaru, shekara 21, mai suna Godwin Raphael dauke da samfurin wayoyin salula daban dabana guda ashirin da shida, da wata karamar bindiga guda daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel