Aiki na kyau: Dakarun Sojin Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram 6 a mafakarsu

Aiki na kyau: Dakarun Sojin Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram 6 a mafakarsu

Dakarun rundunar Sojan kasa ta Najeriya sun samu wata gagarumar nasara akan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a ranar Alhamis 3 ga watan Janairu bayan sun gano wata mafakar mayakan kungiyar, inda suke sansani a kauyukan Gawa da Boskoro cikin karamar hukumar Mafar jahar Borno.

Legit.com ta ruwaito kaakakin rundunar Sojan kasa, Birgediya Sani Usman Kuka-Sheka ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar daya fitar a ranar Alhamis, inda yace Sojoji sun samu nasarar kashe yan ta’adda guda shida, tare da lalata sansanin.

KU KARANTA: Matsalar Boko Haram: Ministan tsaro ya dira garin Maiduguri don gane ma idanunsa

Aiki na kyau: Dakarun Sojin Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram 6 a mafakarsu

Makamai
Source: Facebook

A yayin wannan muhimmin aiki da bataliyar Soji ta 112 daga Birget na 22 ta gudanar, ta gano nakiyoyi guda uku, bindigu hudu, da kuma alburusai da dama, haka zalika sun kama wasu tukunyoyin iskar gas guda biyu tare da kwari da baka.

Duk a cikin nasarar da Sojoji suka samu a wannan samame da suka kai, sun ceto wasu mata guda uku daga sansanin yan book haram dake Boskoro, wanda daga bisani suka mikasu ga jami’an dake kula da sansanin yan gudun hijira na karamar hukumar Dikwa.

Aiki na kyau: Dakarun Sojin Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram 6 a mafakarsu

Sansanin
Source: Facebook

Da yake jinjina na dakarun bataliyar da suka gudanar da wannan aiki, babban kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar BA Akinruloyu ya yaba da jarumtar Sojojin, sa’annan ya bukaci da suka cigaba da kakkabe ragowar yan Boko Haram a duk inda suke.

A wani labarin kuma, babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya kai ma takwaransana rundunar Sojan sama, Sadique Abubakar ziyarar jaje da tayashi alhini bisa hatsarin jirgin yaki na Sojoji da aka samu yayin yaki da yan ta’adda, inda Sojoji hudu suka mutu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel