Ku fara shiga sako-sako ku na kamfe – Buhari ya fadawa ‘Yan APC

Ku fara shiga sako-sako ku na kamfe – Buhari ya fadawa ‘Yan APC

Shugaba Muhammadu Buhari yayi kira ga Matasa da Matan jam’iyyar APC mai mulki, da su shiga yawon yakin neman zabe gida-gida a fadin kasar nan domin ganin sun samu nasara a zaben 2019.

Ku fara shiga sako-sako ku na kamfe – Buhari ya fadawa ‘Yan APC

Buhari yayi kira ga 'yan APC su rika bi gida-gida sun na kamfe
Source: Facebook

Shugaban kasar ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da wani bangare na jam’iyyar APC wanda ke taya shi yakin neman zabe a 2019. An yi wannan ganawa ne a babban dakin taro na Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa a Birnin Abuja.

Buhari ya fadawa Matasa da kuma ‘Yan matan da ke cikin tafiyar APC da su rika bi gida bayan gida su na fadawa jama’a irin kokarin da gwamnatin sa tayi a cikin shekaru 3, tare da kuma bayyana dalilin da ya sa za a bukaci gwamnatin APC ta zarce.

Manema labarai sun bayyana mana cewa wadanda su ka gana da shugaban kasa Buhari sun hada da ‘yan kasuwa, da rikakkun ‘yan siyasa da kuma makada da mawaka, har da kuma tsofaffin jami’an Sojoji da ‘Yan Sanda na Najeriya da su kayi ritaya.

KU KARANTA: INEC ta maidawa Jam’iyyar PDP martani kan shirin murde zaben 2019

Mai dakin shugaban kasa watau Aisha Buhari ce ta jagoranci wannan tawaga inda ta ke kokarin ganin mijin na ta ya zarce a kan karagar mulki. Shugaban kasar dai ya tabbatar da cewa abubuwa za su kara gyaruwa idan har ya zarce kan mulki a 2019 nan.

Shugaban kasar yayi murnar kaddamar da wannan kwamiti na yakin neman zaben sa, inda yayi kira gare su da cewa ka da su yi rauni ko su samu wata karaya wajen ganin Najeriya ta kai ga ci. Buhari ya kuma ce hakan ya nuna matsayin da APC ta ba mata.

Yanzu ana sa rai magoya bayan na APC za su rika shiga lungu-lungu wajen jan hankalin jama’a cewa su marawa jam’iyyar APC baya a zaben da za ayi a watan gobe. Wannan kwamiti zai taimakawa ainihin jirgin yakin neman zaben APC da aka nada kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel