Bayan kalamansa na batanci ga APC, APCn tayi kira da a kama shi da laifin rashawa

Bayan kalamansa na batanci ga APC, APCn tayi kira da a kama shi da laifin rashawa

- Jagoran jam'iyar APC a jihar Adamawa yayi kira ga EFCC da ta gaggauta gurfanar da tsohon SGF a gaban ta

- Duhu yace chairman na EFCC ya gagara gurfanar da Lawan a gaban hukumar tun sanda aka fara tuhumar sa

- Tsohon ciyaman na jam'iyar bangaren arewa ya nemi Shugaban kasa Muhammad Buhari daya tuhumi Magu ko kuma ya sauke shi akan aikin sa idan yanajin tsoron gurfanar da Lawal

Bayan kalamansa na batanci ga APC, APCn tayi kira da a kama shi da laifinn rashawa

Bayan kalamansa na batanci ga APC, APCn tayi kira da a kama shi da laifinn rashawa
Source: Twitter

A ranar Alhamis 3 ga watan Junairu ciyaman din jam'iyar APC na farko na arewa masu gabashin kasar Umar Duhu ya nemi ciyaman na hukumar EFCC daya gurfanar da tsohon sakataren gwamnati ( SGF) Babachir Lawal a gaban hukumar.

Duhu yace baza'a cigaba da tafiya da shugaban EFCC din ba bisa ga nuna gazawar sa akan kama David Babachir Lawal.

DUBA WANNAN: Hasashe: Yadda kabilu, addinai da bangarorin Najeriya zasu yi zaben 2019

Da yake bayani a wani taro a Yola yace an kama Babachir da laifi sannan an cireshi daga SGF amma har zuwa yanzu ba'ayi wani yunkurin gurfanar dashi ba.

Duhu ya bayyana tsoron sa ta hanyar cewa "Idan har EFCC bazata iya gurfanar da Babachir ba to tabbas akwai abinda ke faruwa", wannan ya rage ga shugaban kasa koya sauke shugaban EFCC din ko kuma ya tuhume sa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/de?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel