Buhari ya rantsar da muhimman kwamiti 2 karkashin jagorancin Aisha da Dolapo, hotuna

Buhari ya rantsar da muhimman kwamiti 2 karkashin jagorancin Aisha da Dolapo, hotuna

Da yammacin yau, Alhamis, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamiti biyu da zasu yi masa aikin yakin neman zabensa a tsakanin mata da matasa.

Buhari ya rantsar da kwamitin biyu ne a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya, Abuja.

Aisha Buhari, uwargidan shugaba Buhari, ce zata jagoranci kwamitin yakin neman zabe na mata yayin da Dolapo Osinbajo, uwargidan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, zata jagoranci kwamitin yakin neman zaben Buhari da Osinbajo a tsakanin matasa.

Buhari ya rantsar da muhimman kwamiti 2 karkashin jagorancin Aisha da Dolapo, hotuna

Buhari ya rantsar da muhimman kwamiti 2 karkashin jagorancin Aisha da Dolapo
Source: Facebook

Buhari ya rantsar da muhimman kwamiti 2 karkashin jagorancin Aisha da Dolapo, hotuna

Buhari da Aisha a wurin rantsar da kwamitin yakin neman zabe
Source: Original

Buhari ya rantsar da muhimman kwamiti 2 karkashin jagorancin Aisha da Dolapo, hotuna

Buhari ya rantsar da muhimman kwamiti 2 karkashin jagorancin Aisha da Dolapo
Source: Facebook

Buhari ya rantsar da muhimman kwamiti 2 karkashin jagorancin Aisha da Dolapo, hotuna

Buhari ya rantsar da muhimman kwamiti 2 karkashin jagorancin Aisha da Dolapo
Source: Twitter

Sai dai kamar yadda Legit.ng ta sanar da ku a daya daga cikin labaranta, babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Bola Tinubu da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole basu halarci taron kaddamar da tawagar kamfen wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a yau Alhamis, 3 ga watan Janairu ba.

DUBA WANNAN: Zabe: INEC ta dorawa Amina Zakari alhakin tattara alkaluman sakamakon zaben shugaban kasa

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ce ta jagoranci taron, inda ta sanar da tawagar kamfen din waanda za su yi aikitare da jami’an kungiyar kamfen din shugaban kasar.

An bayyana tawagar kamfen din a matsayin tawagar kamfen din mata da matasa maza don zaben 2019.

An gudanar da taron kadamarwar a Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa Abuja, yan mintina kadan bayan 3pm.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel