An sake kira ga shugaba Buhari da ya sanya damba kan daina Almajirci

An sake kira ga shugaba Buhari da ya sanya damba kan daina Almajirci

- Anyi kira ga yan siyasa dasuyi kokarin kawo karshen almajiranta a kasar

- Wasu mutane sun maida hakan hanyar samun kudin su

- NASFAT zata hada gwiwa da wasu kungiyoyi dan kawo karshen tozarta yara da akeyi

An sake kira ga shugaba Buhari da ya sanya damba kan daina Almajirci

An sake kira ga shugaba Buhari da ya sanya damba kan daina Almajirci
Source: Twitter

Shugaban kungiyar nan ta Nasrul-lahil-l-faith society Abdul'azeez Onike yayi kira ga yan siyasa da suyi kokari wajen kawo karshen almajiranta a arewacin kasar nan.

Onike yayi wannan kira ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a yayin wani taro da NASFAT ta shirya don kawo karshen tozarta yara da akeyi.

"Almajiranta zalunci ne kuma ci da gumin wani ne,sannan ko a musulunce bai halatta ba".

"Wasu mutane sun maida wannan harka hanyar samun kudin su,saboda haka muna kira ga gwamnati data kawo karshen hakan ".

Ya kara da cewa NASFAT zata hada gwiwa da wasu kungiyoyi dan kawo karshen tozarta kananun yara da akeyi.

DUBA WANNAN: Kasashen da jarirai ke son a haife su da inda bassu so a 2019

Yayi kira ga gwamnatin jihohin dasu sanya doka akan kare hakkin kananun yara dan kubutar dasu.

Ya kara da cewa shirin da NASFAT ta fara gudanarwa a shekarar data gabata ya samar da sakamako mai kyau a jihar Calabar da Legas,sannan zasu kara fara gudanar da wani a watan Disemba 2018 wanda zai dauki tsayin watanni Hudu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel