Limamin Coci zai dauki Almajirai ya koya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon

Limamin Coci zai dauki Almajirai ya koya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon

- Kukah Foundation zata horar da almajirai dan inganta rayuwar su

-Kauda almajirai akan hanyoyi yana daya daga cikin abubuwan daya kamata Najeriya ta maida hankali akai

- Ya zama dole yan Najeriya su dunga mutunta junan su dan ganin cigaban kasar

Limamin Coci zai dauki Almajirai ya koya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon

Limamin Coci zai dauki Almajirai ya koya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon
Source: Twitter

A ranar Asabar ne center nan ta Kukah (TKC) ta bayyana kudirin ta na samar da wasu cibiyoyi nata a arewacin kasar dan tallafawa rayuwar almajirai. Almajirai dai wasu yara ne da iyayensu suka yi watsi dasu wai sai dai suyi bara su nema wa kansu abinci.

An sha kushe irin wannan cin zarafin yara da sunan karatun Kur-Ani, amma babu wata hukuma da ta iya daukar mataki a kai.

Limamin Kirista na Catholic Diocese dake jihar Sokoto Rev Matthew Kukah ne ya bayyana hakan a yayin da suke gudanar da wani taron karawa juna sani mai taken "Interfaith dialogue and engagement for Christians and muslims" wanda ya gudana a Minna.

Taron wanda ya samu halartar manyan limaman kiristoci dana musulunci daga Niger, Kano, Gombe da kuma jihar Yobe .

Kukah yace mafi yawan matsalolin da ake fama dasu a yankunan mu zai ragu idan aka bawa wadannan yara muhimmanci da kulawa.

DUBA WANNAN: Abubuwan da Allah zai yi da Najeriya a bana 2019 - kungiyar CAN

"Kautar da wadannan yara daga tituna yana daya daga cikin abinda ya kamata Najeriya ta sanya a gaba".

"Nan bada jimawa ba kungiyar zata sanya hannu akan wata yarjejeniya da fahimta da abokan hulda na kasashen ketare dan kawo karshen almajiranta".

Shekara guda kenan ana wannan shiri na Kukah Foundation, amma kuma MURIC, wata kungiya ta Muslim Rights Council, tace sam bata yarda ba.

MURIC din dai, ba'a taba jinta ba a wajen kare hakkin Almajiran, ko wajen iliminsu na Boko ko bangaren abinci da sana'a, sai yannzu da suka ji wani zai agazawa miliyoyin almajirai, suka ce sam, ba zai yiwu ba.

Watakil suna tsoron kada yaran sufara sha'awar addinin da ya tallafa musu ne, watau kiristanci, maimakon wanda yayi watsi dasu ya maiida su mabarata. A nan sai dai muce kukan kurciya ai jawabi ne, mai hankali ke ganewa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel