Atiku ya bukaci daya daga cikin gwamnonin APC ya yi murabus, ya bayyana dalili

Atiku ya bukaci daya daga cikin gwamnonin APC ya yi murabus, ya bayyana dalili

- Dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya yi kira da Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya yi murabus daga kujerarsa

- Atiku ya ce tunda har gwamnan ya amsa cewa ya gaza kiyaye rayuka da dukiyoyin al'ummar jiharsa babu amfanin ya cigaba da kasancewa gwamna

- Atiku ya kuma yi gargadin cewa saka dokar ba zai kawo sauki ne kawai na kankanin lokaci saboda haka ya dace a binciko ainihin abinda ke janyo rikice-rikice a jihar

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce yana maraba da duk wani mataki da gwamnatin tarayya za ta dauka domin kawo karshen kashe-kashe a jihohin Zamfara, Katsina amma ya yi gargadin cewa saka dokar zai kawo sauki ne kawai na dan kankanin lokaci amma ba zai magance ainihin matsalar ba.

Atiku ya bukaci daya daga cikin gwamnonin APC ya yi murabus, ya bayyana dalili

Atiku ya bukaci daya daga cikin gwamnonin APC ya yi murabus, ya bayyana dalili
Source: Twitter

A martanin da ya mayar jan kiran da Gwamna Abdul-Aziz Yari ya yi na neman a saka dokar ta baci ta bakin mai magana da yawunsa Phrank Shuaibu, Atiku ya ce dole a gano abinda ke haifar da rikici-rikicen a magance shi kafin a samu zaman lafiya mai dorewa.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC ta ce tana tausayin wani gwamnanta

Sanarwar ta ce gaggawar da gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara keyi na saka dokar ta bacin ya nuna yadda suke son ganin sun samu kuri'a a jihohin a babban zaben 2019 ta kowanne hali.

"Yarjejeniyar da aka cimma a Aso Rock Villa abu mai sauke ne: Gwamnatin tarayya zata saka dokar ta baci wadda hakan zai bawa APC damar fitar da dan takarar gwamna a jihar wadda ta gaza yi cikin wa'adin da INEC ta bayar," inji sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.

Atiku ya ce wannan ya nuna cewa Shugaba Buhari yana son yin duk mai yiwuwa ne domin ganin jam'iyyarsa tayi galaba a jihohin Zamfara da Katsina.

Duk da haka, Atiku ya ce wannan ba shine zai sanya APC tayi nasara ba saboda al'umma ne ke kada kuri'a ba gwamnan jihar Zamfara ko shugaban kasa ba.

Ya kuma yi kira ga Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya yi murabus daga mukaminsa tunda ya amince ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel