Kungiyar musulunci ta bukaci gwamnati ta kawo karshen almajiranci

Kungiyar musulunci ta bukaci gwamnati ta kawo karshen almajiranci

- Kungiyar musulunci na NASFAT ta roki gwamnati ta kafa dokokin da za su kawo karshen alamjiranci a Najeriya

- NASFAT ta ce almajiranci bayan cikin koyarwar addinin musulunci kuma yana jefa yara kanana cikin hadari

- NASFAT ta ce a shirye ta ke tayi aiki da 'yan majalisun jiha da na tarayya domin kafa dokoki da za su kawo karshen almajiranci

Shugaban da'awah na kunfiyar Nasrul-Lahi-L-Faith Society (NASFAT), Abdulazeez Onike ya yi kira ga gwamnati da taimaka wurin kawo karshen keta hakkin yara da akeyi ta hanyar almajiranci a wasu sassan arewacin Najeriya.

Onike ya yi wannan kirar ne a yayin da ya ke hira da manema labarai a yayin wani taro da NASFAT ta shriya domin kawo karshen keta hakkin yara a Najeriya kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kungiyar musulunci ta bukaci gwamnati ta kawo karshen almajiranci

Kungiyar musulunci ta bukaci gwamnati ta kawo karshen almajiranci
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC ta ce tana tausayin wani gwamnanta

"Almajiranci ba koyarwan musulunci ba ne kuma zalunci ne. Babu zalunci a cikin addinin musulunci.

"Wasu mutane sun mayar da shi hanyar samun abincinsu; saboda haka muke rokon gwamnati ta taimaka domin kawo karshen almajiranci," inji malamin na addinin musulunci.

A farko cikin wa'azinsa, shugaban NASFAT, ya ce Manzon Allah SAW yana kaunar yara sosai har a wani lokaci ya tswaita sujuda har sai da jikokinsa suka sauka daga bayansa.

Ya ce NASFAT tana hadin gwiwa da wasu kungiyoyi domin ganin ta kawo karshen cin zarafin yara da akeyi a wasu sassan Najeriya.

Shugaban NASFAT, Kamil Bolarinwa ya yi kira da gwamnati ta rika aiwatar da dokokin kiyaye hakkin yara da ake dashi a kasar tare da karfafa su domin kawo karshen cin zarafin yara.

"A shirye NASFAT ta ke tayi aiki da 'yan majalisun jihar da tarayya domin kafa sabbin dokoki da za su kare hakkin yara," inji shi.

Ya yabawa USAID da UNICEF saboda tallafin da suke bawa NASFAT a yunkurinsu na kawo karshen almajiranci a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel