Zabe: Ba zamu janye yajin aiki ba - ASUU

Zabe: Ba zamu janye yajin aiki ba - ASUU

A yau, Alhamis, ne kungiyar malaman jami'o'n Najeriya (ASUU) ta bayyana cewar ba zata janye yajin aikin da take yi ba saboda zabukan shekarar nan da za a fara a watan Fabrairu ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu, na cewa yajin aikin ASUU zai shafi zabukan shekarar 2019.

Sai dai yayin wata hira da shugaban kungiyar ASUU reshen jami'ar Ibadan, Dakta Deji Omole, a yau Alhamis, ya ce babu ruwansu da zabukan da hukumar INEC zata gudanar.

Omole ya ce kungiuar ASUU a shirye take ta cigaba da yajin aiki har sai bukatarta ta biya ko da maganar zabe ko sabanin haka.

Zabe: Ba zamu janye yajin aiki ba - ASUU

Taron ASUU
Source: UGC

Ya kara da cewa INEC na iya daukan ma'aikatan wucin gadi daga miliyoyin 'yan Najeriya da suka cancanta.

"Babu ruwanmu da INEC, saboda zasu iya nemo ma'aikata na wucin gadi da zasu yi masu aikin zabe.

"Damuwar 'yan Najeriya shine a gudanar da zabe sahihi na adalci, ba wai shigar malaman jami'o'i ba.

DUBA WANNAN: Zabe: INEC ta dorawa Amina Zakari alhakin tattara sakamako

"Koda babu yajin aikin ASUU ba duk malaman jami'a ne zasu yi aiki da hukumar INEC lokacin zabe ba. Ko a baya hukumar INEC na aika takarda ga malaman da take so suyi mata aiki ne, ba ASUU suke aikowa takarda ba," a kalaman Omole.

Shugaban na ASUU ya bukaci jama'a su cigaba da matsawa gwamnatin tarayya domin ta zuba isassun kudade a bangaren ilimi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel