Ya zama dole yan Najeriya su yi waje da APC – Shehu Sani

Ya zama dole yan Najeriya su yi waje da APC – Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani, sanata ya bukaci yan Najeriya da su yi waje da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar 16 ga watan Fabrairu

- Sani ya yi zargin cewa gwamnatin APC ta haddasa wa mutane barna sosai

- Ya ce ba ta cancanc a sake basu dama a karo na biyu ba

Shehu Sani, sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya bukaci yan Najeriya da su yi waje da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Da yake jawabi ga kungiyar matasan Igbo wato Igbo Youth Peace and Unity Initiative a Kaduna a yammacin ranar Laraba, 2 ga watan Janairu, Sani ya yi zargin cewa gwamnatin APC ta haddasa wa mutane barna sosai.

Za a gudanar da zaben yan takarar shugaban kasa da na majalisar dokoki a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Ya zama dole yan Najeriya su yi waje da APC – Shehu Sani

Ya zama dole yan Najeriya su yi waje da APC – Shehu Sani
Source: Depositphotos

“Kada mu yaudari kanmu, ya zama dole mu fadawa kanmu gaskiya, kasar nan bata da lafiya, jihar bata da lafiya. Yn Najeriya sun tsimayi samun zaman lafiya fiye da yadda yake a yanzu. Mutanen da suke ta rokonku akan ku zabe su a shekaru uku da rabi da suka gabata sun mayar da kansu tamkar ubangiji,” inji Sani.

KU KARATA KUMA: Ba zan ba yan Najeriya kunya ba – Buhari

“Mun ga yadda talauci ya hargitsa rayuwar yan Najeriya a shekaru uku da rabid a suka gabata, mun ga kashe-kashe, zubar jini da tashe-tashen hankula, mun ga rabuwar kai, mun ga yadda gwamnan jihar ya kori dubban ma’aikata.

“Ta yaya a duniyan nan za a sake ba mutumin da bai da tausayin jama’a wata dama, wanda bai da zuciyar tausayi.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel