Ba a ga Tinubu da Oshiomhole ba yayinda Buhari ya kaddamar da tawagar kamfen

Ba a ga Tinubu da Oshiomhole ba yayinda Buhari ya kaddamar da tawagar kamfen

- Babban jigon APC, Bola Tinubu da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole basu halarci taron kaddamar da tawagar kamfen da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ba a yau

- Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ce ta jagoranci taron

- Aisha ce ke jagorantar kungiyar yayinda uwargdan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo ce mataimakiya

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Bola Tinubu da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole basu halarci taron kaddamar da tawagar kamfen wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a yau Alhamis, 3 ga watan Janairu ba.

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ce ta jagoranci taron, inda ta sanar da tawagar kamfen din waanda za su yi aikitare da jami’an kungiyar kamfen din shugaban kasar.

Ba a ga Tinubu da Oshiomhole ba yayinda Buhari ya kaddamar da tawagar kamfen

Ba a ga Tinubu da Oshiomhole ba yayinda Buhari ya kaddamar da tawagar kamfen
Source: Twitter

An bayyana tawagar kamfen din a matsayin tawagar kamfen din mata da maza don zaben 2019.

An gudanar da taron kadamarwar a Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa Abuja, yan mintina kadan bayan 3pm.

KU KARANTA KUMA: Zabe: INEC ta dorawa Amina Zakari alhakin tattara sakamako

Uwargdan shugaban kasa, Aisha ce ke jagorantar kungiyar yayinda uwargdan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo ce mataimakiya.

Uwargidan Buhari dai ta soki APC da Mista Oshiomhole kan yadda aka gudanar da zaben fdda gwanin jaiyyar a fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel