Rundunar soji ta kama mutane 71 a jihar Adamawa

Rundunar soji ta kama mutane 71 a jihar Adamawa

A cigaba da kokarinta na kwantar da tarzoma, dakarun sojin Najeriya na runduna ta 23 dake garin Yola, babban birnin jihar Adamawa, sun kama wasu mutane 71 da ake zargi na da hannu a rikicin da ya barke tsakanin garuruwan Lunguda da Waja a Guyuk ta karamar hukumar Lamurde.

Birgediya janar Bello Abdullahi, kwamandan rundunar sojin da ya jagoranci ofireshon din kama mutanen, ya sanar da hakan a yau, Alhamis, yayin mika mutanen ga rundunar 'yan sanda.

Abdullahi, ya kara da cewar an kara tura wasu dakarun soji zuwa yankin domin kara tabbatar da cewar wani rikicin bai kara barkewa ba tare da bayyana cewar sun yi nasarar kama wasu makamai da suka hada da bindigu, kwari da baka, adda, da wukake a wurin wadanda suka kama.

Da yake jawabi a kan muhimmancin zaman lafiya a tsakanin kabilun jihar, Abdullahi ya ce rundunar soji a shirye take ta dauki matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya.

Rundunar soji ta kama mutane 71 a jihar Adamawa

Dakarun rundunar soji
Source: Depositphotos

Kazalika ya nemi hadin kan jama'a domin bawa dakarun sojin damar tabbatar da zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

An yi asarar amfanin gona da gidaje yayin rikicin.

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar hukumar sojin saman Najeriya (NAF) ta sanar da cewa matukan jirginta biyu da wasu sojoji uku ne suka rasu sakamakon hatsarin jirgi mai saukan angulu yayi a daren Laraba yayin yaki da Boko Haram.

DUBA WANNAN: Fashin Offa: Ka daina rawa a kan kabarin mamata - Lai Mohammed ya karyata Saraki

TheSun ta ruwaito cewa jirgin mai saukan angulu kirar Mi-35M ya yi hatsari ne yayin da ya ke tallafawa dakarun sojin Najeriya na Bataliyar 145 a garin Damasak da ke jihar Borno.

Mai magana da yawun sojin saman Najeriya, Air Commodre Ibikunle Daramola ya bayyana sunayen wadanda suka rasu kamar haka, Flight Laftanat Perowei Jacob; Flight Laftanat Kaltho Paul Kilyofas; Saja Auwal Ibrahim; Lance Corporal Adamu Nura da Meshack Ishmael.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel