Farashin man fetur yana wala-wala a kasuwar Duniya, ya sauko zuwa $53

Farashin man fetur yana wala-wala a kasuwar Duniya, ya sauko zuwa $53

Mun samu labari cewa farashin gangar danyen man fetur ya na cigaba da sauka kasa a kasuwannin Duniya. Yanzu gangar mai ya koma Dala $53 bayan farashin man ya haura har Dala 85 a shekarar bara.

Farashin man fetur yana wala-wala a kasuwar Duniya, ya sauko zuwa $53

Kwanakin baya sai da farashin man fetur ya koma $48
Source: Depositphotos

Ana cigaba da samun wala-wala a kasuwar man fetur ta Duniya bayan da gangar danyen fetur ya karye a cikin ‘yan kwanakin nan, Man fetur na Najeriya watau Bonny Light shi ne wanda ya fi kowane kasuwa a halin yanzu.

Gangar man fetur din West Texas da su WTI da OPEC Basket su na kan Dala $45 zuwa $53 ne a kasuwannin mai na Duniya. Ragargajewar farashin man fetur din yana iya jefa tattalin arzikin Najeriya cikin wani hali.

KU KARANTA: An yi sama da fadi da kudin tsaro cikin kudin yakin neman zabe - PDP

Man fetur din Najeriya wanda yana cikin wanda ya fi daraja a kasuwa ya fadi ne da kusan kashi 8%. Fetur din Amurka kuwa ya ruguje da fiye da kashi 40% a cikin mako nan. Amurka ta ji dadin faduwar farashin man.

Najeriya tayi kasafin 2019 ne a kan Dala $60, an samu karyewar tattalin arzikin ne bayan irin su Saudiyya ta rage adadin man da ta ke hakowa. Hakan kuma bai rasa nasaba da sauka kasa da darajar Dalar Amurka tayi.

Ana tunani shugaban kasar Amurka, Donald Trump, yana cikin wanda su kayi sanadiyyar karyewar farashin man. Donald Trump yace hakan zai zo wa mutanen kasar Amurka da sauki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel