Ba zan ba yan Najeriya kunya ba – Buhari

Ba zan ba yan Najeriya kunya ba – Buhari

- Shugaba Buhari ya sha alwashi cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba

- Ya dauki wannan alkawarin ne a wajen taron karramawa na kafofin watsa labaran Najeriya da aka yi a fadar shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashi cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba wajen sawa al’umman kasar daga wurare daban-daban da suka bashi yardarsu.

Shugaban kasar yayi Magana ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu a fadar shugaban kasa da ke Abuja a wajen taron karramawa na kafofin watsa labaran Najeriya wato Nigerian Media Merit Award wanda kwamitin amintattu na kungiyar karrama kafofn watsa labarai ta shirya.

Ba zan ba yan Najeriya kunya ba – Buhari

Ba zan ba yan Najeriya kunya ba – Buhari
Source: Depositphotos

Ya yaba ma kokarin kungiyar sannan ya kara da cewa dama chan ya san mambobin kungiyar NMMA da dama tun ma kan ya san cewa zai kasance a wurin.

Tsohon Darakta Janar na gidan talbijin din Najeriya (NTA), Mista Vincent Maduka wanda ya jagorancin trawagar yace Buhari ya cancanci zama zakarar shekara “saboda kana mutunta hakkin kafofin watsa labarai ba tare da kowani shamaki ba”.

KU KARANTA KUMA: Zabe: INEC ta dorawa Amina Zakari alhakin tattara sakamako

Ya bayyana cewa a karkashin Buhari babu kafar watsa labarai da aka rufe, sannan kuma an bayar da lasisin talbijin din makaranta na farko ga jami’ar Lagas, karkashin jagorancin shahararren malamin bangaren karatun jarida, Farfesa Ralph Akinfeleye.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel