Mambobin APC 500 sun sauya sheka PDP

Mambobin APC 500 sun sauya sheka PDP

- Hon. Sergius Oseasochie Ogun, da ke wakiltan Esan ta kudu masa gabas, Esan ta arewa maso gabas a majalisar wakilai ya kaddamar da aikin ruwan sha ga al’ummansa

- A wajen kaddamar da aikin mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 500 ne suka sauya sheka zuwa Peoples Democratic Party (PDP)

- Ogun yace hakan na daya daga cikin alkawaran yakin neman zabe da ya daukar ma mutanensa

Al’umman garin Emu da ke karamar hukumar Esan ta kudu maso gaas a jihar Edo sun shiga samuwar shekara a sa’a yayinda Hon. Sergius Oseasochie Ogun, da ke wakiltan Esan ta kudu masa gabas, Esan ta arewa maso gabas a majalisar wakilai ya kaddamar da aikin ruwan sha a yankin.

Mambobin APC 500 sun sauya sheka PDP

Mambobin APC 500 sun sauya sheka PDP
Source: Depositphotos

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka shirya biki domin tarban mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 500 da suka sauya sheka zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

Dan majalisan ya gina famfon ruwa a garin Emu ne domin magance matsalar rashin ruwa da yankin ke fama dashi.

KU KARANTA KUMA: Abunda zan yi a lokacin zaben 2019 - Obasanjo

Yayinda yake kaddamar da aiki, Ogun yace hakan na daya daga cikin alkawaran yakin neman zabe da ya daukar ma mutanen sannan ya bkaci da su yi amfani dashi yadda ya kamata, yayinda tya kuma bukaci da su kare aikin daga barayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel