Fadar Aso Rock ta sake gwale 'yan PDP kan batun tallafin jari daga kudaden Abacha

Fadar Aso Rock ta sake gwale 'yan PDP kan batun tallafin jari daga kudaden Abacha

- Fadar shugaban kasa tace abin haushi ne da Fayose ke kalubalantar shirin Tradermoni

- Shirin dai anyi shi ne don taimokon yan kasuwa masu karamin karfi

- Hakan na nuna burin fadar shugaban kasan gurin tallafawa masu karamin karfi

Fadar Aso Rock ta sake gwale 'yan PDP kan batun tallafin jari daga kudaden Abacha

Fadar Aso Rock ta sake gwale 'yan PDP kan batun tallafin jari daga kudaden Abacha
Source: Depositphotos

Fadar shugaban kasa tace abin haushi ne da tsohuwar gwamnatin jihar Ekiti karkashin Ayo Fayose ke kalubalantar Tradermoni.

Tradermoni dai wani wata cibiya ce da ke rantawa kananan yan kasuwa kudi har Naira dubu goma ba tare da sun bada riba ba. Shirin na gwamnatin tarayya ne.

Fayose ya kwatanta shirin da hanyar kaikaicewa gurin kara kwashe kudin da Abacha ya kwashe yayin mulkin shi wanda gwamnatin Switzerland ta dawo dasu.

Kungiyar maida martani ta SIP a wata maganar ta a Abuja tace ba daya ba ,ba biyu ba ana yin bayanin shirin Tradermoni ga mutane.

Raba kudin Tradermoni din a bayyane ake yi, babu boye boye.

DUBA WANNAN: Abubuwan da Allah zai yi da Najeriya a bana 2019 - kungiyar CAN

"Abin haushi ne da jam'iyyar PDP da kuma Fayose suke cigaba da yada karya da karairayi. Wannan na nuna cewa Fayose da mukarraban shi basu da ma abinda zasu yi yakin neman zabe dashi. Don haka je suka zage gurin hada zargi irin wannan."

Fadar shugaban ta tabbatar da cewa Shirin Tradermoni an kirkiro shi ne don taimakon rayuka da kasuwancin yan Najeriya masu matsakaicin karfi.

Shirin na nuna cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tsaya gurin maida hankali gurin samar da cigaban yan kasar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel