Zabe: INEC ta dorawa Amina Zakari alhakin tattara sakamako

Zabe: INEC ta dorawa Amina Zakari alhakin tattara sakamako

Amina Zakari, kwamishiniya a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta samu mukamin shugaban mai kula da tattara sakamako a cibiyar tattara sakamako zabukan zaben shekarar nan.

A yau, Alhamis, ne INEC ta nada Amina a matsayin wacce zata jagoranci kwamitin tattara sakamakon zabe, daya daga cikin kwamiti biyu da hukumar zaben ta kafa a cigaba shirye-shiryenta na tunkarar zabe a watan Fabrairu.

Da yake rantsar da kwamitin, Farfesa Mahmoud Yakubu, shugaban hukumar INEC, ya ce kwamitin da Amina zata jagoranta ne keda alhakin tattara alkaluman sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi.

INEC ta ware wuri na musamman da kwamitin zai yi amfani da shi domin tattara alkaluman sakamakon zaben shugaban kasa. Wurin zai zama sakatariyar kwamitin.

Zabe: INEC ta dorawa Amina Zakari alhakin tattara sakamako

Amina Zakari
Source: Twitter

Shugaba Buhari ya taba nada Amina a matsayin shugabar hukumar INEC ta rikon kwarya.

Jam'iyyar PDP mai adawa ta yi korafi a kan nada Amina a matsayin shugabar INEC tare da bayyana cewar tana da alaka ta jini da shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: Muna son biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi amma akwai wata matsala - Gwamnonin Najeriya

Kola Ologbondiyan, kakakin jam'iyyar PDP, ya taba bayyana cewar, "bamu yarda da shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ba a dangane da batun gudanar da zabe na adalci a shekarar 2019 ba, kuma ba zamu amince da bawa Amina Zakari wani aiki da ya shafi zabe ba saboda kowa ya san cewar tana da alaka ta jini da Buhari."

Kwamitin tattara sakamakon zaben yana da mambobi daga wasu hukumomi na ma'aikatun gwamnatin tarayya da kuma hukumomin tsaro, kuma aikinsu zai kasance bisa tsare-tsaren dokokin zabe na INEC, kamar yadda Farfesa Yakubu ya bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel