Muhimman abubuwa da su auku a Majalisar Tarayya a shekarar bara

Muhimman abubuwa da su auku a Majalisar Tarayya a shekarar bara

A daidai lokacin da aka shiga sabuwar shekara, mun kawo maku wasu muhimman abubuwa da su ka faru a Majalisar wakilai na tarayyar Najeriya a shekarar da ta gabata. A bara ne dai shugabannin Majalisar su ka sauya-sheka zuwa PDP.

Muhimman abubuwa da su auku a Majalisar Tarayya a shekarar bara

Shugaba Buhari gaban 'Yan Majalisar Tarayya yana gabatar da kasafin kudi
Source: UGC

Daga cikin manyan abubuwan da su ka faru kamar yadda Premium Times ta kawo su akwai:

1. Dawo da Abdulmumin Jibrin bakin aiki

A shekaran da ta wuce ne aka yi wa ‘Dan Majalisar Kiru da Bebeji watau Honarabul Abdulmumin Jibrin afuwa ya koma bakin aikin sa, bayan an dakatar da shi bisa zargin shugabannin majalisar da yayi da cushe cikin kasafin kudin kasar.

2. Aikawa Shugaban kasa sammaci

A cikin watan Afrilu ne Majalisar kasar ta aikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari sammaci a dalilin kashe-kashe da ya zama ruwan dare a Najeriya. ‘Yan Majalisar sun kuma yi ikirarin rufe Majalisar na kwanaki 3 domin nuna rashin jin dadin su.

KU KARANTA: Za a kashe fiye da Biliyan 7 a kan jiragen saman fadar shugaban kasa a 2019

3. Zargin Mataimakin Shugaban kasa

Majalisar kasar ta kuma zargi Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da sa hannu wajen karkatar da wasu kudi daga asusun hukumar NEMA. Wani ‘Dan Majalisa daga Gombe ya gudanar da bincike inda yace an yi awon gaba da Biliyan 5.

4. Sauya-sheka daga APC zuwa PDP

A karshen Watan Yuli ne shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da mukarraban sa su ka fice daga APC zuwa PDP. Kafin nan wasu ‘yan majalisar sun tsere daga APC a tsakiyar shekarar. Wannan sauya-sauyen sheka ya girgiza jam’iyyar.

5. Gabatar da kasafin kudin 2019

A cikin Watan Disamba kuma shugaban kasa Buhari ya gabatar da kundin kasafin kudin shekarar bana. Sai dai kuma ‘yan majalisar hamayya sun ta yi masa ihu a lokacin da yake jawabi. A karshe dai aka tashi baram-baram tsakanin ‘yan PDP da APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel