Dan Adam ya sake kafa tarihi a safiyar yau, an sake sauka kan wata

Dan Adam ya sake kafa tarihi a safiyar yau, an sake sauka kan wata

- Kasar China ta turo na'ura ta farko da ta sauka a gefen wata

- Na'urar ta sauka ne a ranar alhamis, karfe 10:26 am agogon Beijing

- China ce kasa ta uku da ta sauka a duniyar wata bayan US da Rasha a duniya

Dan Adam ya sake kafa tarihi a safiyar yau, an sake sauka kan wata

Dan Adam ya sake kafa tarihi a safiyar yau, an sake sauka kan wata
Source: Twitter

A tarihi na farko, Kasar China ta tura na'ura ta farko da ta sauka a can gefen wata, inji kafar yada labarai ta Chinese a ranar alhamis ta fada. CNSA ce ta saukar da na'urar mai suna Change 4 da karfe 10:26 am agogon Beijing a ranar alhamis, a South Pole-Aitken Basin kamar yanda CCTV ta ruwaito.

Dan Adam ya sake kafa tarihi a safiyar yau, an sake sauka kan wata

Dan Adam ya sake kafa tarihi a safiyar yau, an sake sauka kan wata
Source: Twitter

Na'urar tayi saukar karshe akan kilomita 15 saman wata kamar yanda wanda ya hada Chang'e 4, Sun Zezhou ya fada.

Kafafen yada labarai sun ce na'urar ta fara bada hoto mafi kusa na can bangaren wata. Bayan sa'o'i shida da sauka, na'urar zata sauka zuwa saman wata kamar yanda Yu Guobin ya sanar da CCTV.

Dan Adam ya sake kafa tarihi a safiyar yau, an sake sauka kan wata

Dan Adam ya sake kafa tarihi a safiyar yau, an sake sauka kan wata
Source: Twitter

Bangaren watan shine bangaren da bai taba kallo duniya ba saboda juyin watan. Ana kiranshi wani lokaci da "Bangaren duhu na watan," duk da yana samun isasshen hasken rana kamar sauran bangaren dake fuskantar rana.

"China na kan hanyar zama kasa mai karfi a ilimin sararin samaniya. Kuma wannan alama ce babba," inji shugaban makera na'urar, Wu Weiren, ya sanar da CCTV.

Na'urar Chan'ge 4 na da tsawon meter 1.5 da kusan fadin meter 1 da tayoyi 6.

DUBA WANNAN: Sabbin bincike na kira ga masu ciki da masu shayarwa su guji shan Zobo

"Kasar China ta kosa ta shiga cikin littafin tarihin nasarorin sararin samaniya," inji Joan Johnson-Freese, farfesa a kwalejin sojin ruwa dake US kuma kwararre a shirin sararin samaniya na China.

Kasar ta sanar da tabbacin saukar na'urar bayan da bai wuce sa'a daya ba da China Daily da China Global Television Network ta goge rubutun cewa na'urar ta samu nasarar sauka. Mutane sun kasa gane gaskiyar zancen domin babu cikakken bayanin dalilin da yasa suka goge rubutun a shafin tuwita.

Na'ura ta karshe da ta sauka a duniyar wata mai suna Yutu, or Jade Rabbit ta dena aiki ne a watan Augusta 2016 bayan kwanaki 972 da tayi a duniyar wata a cikin shirin saukar Chang'e 3.

China ce kasa ta uku da ta sauka a duniyar wata bayan US da Rasha.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel