Siyasar Coci ta Father Mbaka: Bayan da yace kar zabi Buhari a 2019 a bara, yanzu kuma yace a zabe shi, sharhi

Siyasar Coci ta Father Mbaka: Bayan da yace kar zabi Buhari a 2019 a bara, yanzu kuma yace a zabe shi, sharhi

- Buhari ya cancanci mu bashi goyan baya akan yaki da rashawa

- Muna mika godiyar mu a gareshi saboda shine mutumin daya fahimci halin da muke ciki

- Yayi kira ga yan Najeriya dasu kadawa Buhari kuri'un su a zaben dazai gudana a watan Fabrairu

Siyasar Coci ta Father Mbaka: Bayan da yace kar zabi Buhari a 2019 a bara, yanzu kuma yace a zabe shi, sharhi

Siyasar Coci ta Father Mbaka: Bayan da yace kar zabi Buhari a 2019 a bara, yanzu kuma yace a zabe shi, sharhi
Source: Depositphotos

Sanannen Malamin cocin Catholica, wanda yayi kaurin suna a 2014, bayan da ya zama babban jigo a kokarin masu zaben 2015 na kayar da GEJ ya sake baara.

Ejike Mbaka ya bayyana goyan bayan shi ga shugaba Muhammad Buhari, sannan yayi kira ga 'yan Najeriya dasu kada masa kuri'un su a zaben dazai gudana a watan Fabrairu.

Sai dai masu sharhin siyasa na ganin Limamin ya fiye katsalandan a harkokin siyasa, inda kuma a baya ya sosoki gwamnatin APC yama ce kada a sake a sake zabar Buharin, domin kuwa babu alamar cewa shi yake mulki musamman lokutan da yake rashin lafiya.

An kuma jiyo Mbaka, yana kuma caccakar Mr. Peter Obi a watannin baya, wai saboda da ya ziyarci Cocinsa bai ajje sadaqa ba, kamar yadda ake sa rai zaiyi, nan ma saida uwar coci ta duniya tace lallai ba da yawunta ake ba.

Sai yanzu kuma, Mr Mbaka ya bayyana cewa Buhari ya kamata a zaba a 2019, ya kuma hakan ne a ranar Talata yayin da yake mika sakon barka da shigowa sabuwar shekara "Duk wani shugaba da zaiyi yaki da cin hanci da rashawa ya cancanta mu bashi goyan baya".

DUBA WANNAN: Illoli da alfanun shan maganin takaita haihuwa da kiyayyar daukar ciki

Mbaka wanda yaki bada fuskar ayi suka kan goyan bayan Buhari yayi kira ga yan Najeriya dasu dage da addu'a don samun nasarar kasar.

"Muna yiwa Buhari addu'a saboda shine mutumin daya fuskanci halin da muke ciki,tunda aka kirkiri Najeriya bamu taba ganin shugaban daya bunkasa harkar noma da kiwo ba sai shi.

"Shekaru 16 da suka gabata hanyar Anambra zuwa Enugu ta lalace amma cikin shekaru 4 ya gyara wadannan hanyoyi da kuma hanyar Umuahia.Allah ya saka masa da alkhairi.

"Shekaru Hudu ba shekaru Takwas bane,ya gama da shekaru hudun sa saboda haka inayi masa fatan samun nasara akan ya dawo ya karashe ragowar Hudun."

Aduk sanda bashi da lafiya munayi masa addu'a kuma Allah yana amsawa wajen bashi lafiyar, ubangiji ne kadai yasan dalilin barinshi a raye da baya bukatar shi da ya dade da dauke shi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel