Ya hallaka kansa saboda abin da matarsa tayi masa a Legas, zaku iya duba me ya hado su a ciki

Ya hallaka kansa saboda abin da matarsa tayi masa a Legas, zaku iya duba me ya hado su a ciki

- Wani DJ ya hallaka kansa bayan ya watsa sakon bankwana a shafinsa na Instagram

- Ya hallaka kanshi ne a ranar Laraba 2 ga watan Junairu shekara ta 2019

- Ya nemi duk wani masoyin shi daya sanya farin kaya saboda shine kalar dayafi so

Ya hallaka kansa saboda abin da matarsa tayi masa a Legas, zuko iya duba me ya hado su a ciki

Ya hallaka kansa saboda abin da matarsa tayi masa a Legas, zuko iya duba me ya hado su a ciki
Source: UGC

Hallaka kai dai abu ne da kan zo wa jama'a da abin tausayi da jimami, wasu sukan gwammace su halaka kansu maimakon su fuskanci kalubalen dake gabansu, kwararru sun ce ya kamata a dinga kula da wadanda aka lura sun shiga damuwa.

Shahararren mai bada kida a Najeriya, Seun Omogaji wani DJ mazaunin Legas wanda akafi sani da Djxgee ya rasu.

Rahoton yan sanda ya bayyana cewa Djxgee yace zai kashe kansa a ranar Laraba 2 ga watan Junairu.

Ya sha maganin kwari ne mai suna "Sniper" bayan samun matsala da sukayi da matar shi.

DUBA WANNAN: Aiki jaa a gaban Arewa, dubi yadda yawan talakawa da yake a jiha-jiha, kudu da arewa

Kafin rasuwar tashi ya watsa sakon bankwana a shafinsa na Instagram inda ya nemi masoyan sa da su nuna jimamin mutuwar sa ta hanyar sanya fararen tufafi saboda fari shine kala mafi soyuwa a gareshi.

Kamar yadda ya rubuta "akwai wani abun girmamawa da mutane kiyiwa duk wani masoyin su daya rasu".

"Mutane na saka bakaken tufafi dan nuna alhinin su a bisa rashin da sukayi,amma ni ina rokon ku da ku sanya farare saboda itace kala mafi soyuwa a gareni ".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel