Abunda zan yi a lokacin zaben 2019 - Obasanjo

Abunda zan yi a lokacin zaben 2019 - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa rawar ganin da zai taka zai kasance kamar na mai tsaro

- Ya ce zai kasa ya tsare sannan ya sanar a duk inda aka samu rashin gaskiya

Yayinda yan Najeriya ke shirin fara zaben shugaban kasa a wata mai zuwa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa rawar ganin da zai taka zai kasance kamar na mai tsaro, wanda zai kasa ya tsare sannan ya sanar a duk inda aka samu rashin gaskiya.

Abunda zan yi a lokacin zaben 2019 - Obasanjo

Abunda zan yi a lokacin zaben 2019 - Obasanjo
Source: UGC

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayinda ya ke jawabi ga tawagar jam’iyyar Democratic Party (ADP), karkashin jagorancin dan takarar shugaban kasar ta, Yabaji Sani, a ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu a Abeokuta.

A wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan labarai na kungiyar kamfen din YY San, Pam Ibrahim, tsohon shugaban kasar ya bkaci yan Najeriya da su zabi shugabannin da suka cancanta bisa tafarkin damokradiyya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan takarar gwamna 16 sun lamunce ma dan takarar APC a Cross River

Jigon kasar, wanda ya sha sukar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai ci a yanzu, ya yi imanin cewa Najeriya na kan hanya mai dauke da rukuni uku sannan ya nuna burin cewa jam’iyyar ADP na kan hanyar wannan tafiya kuma za ta samar da shugabanci nagari duba ga mambobinta, musamman a irin wannan lokaci da yan Najeriya ke neman shugabanci nagari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel