Yanzu Yanzu: Yan takarar gwamna 16 sun lamunce ma dan takarar APC a Cross River

Yanzu Yanzu: Yan takarar gwamna 16 sun lamunce ma dan takarar APC a Cross River

- Yan takarar gwamna 16 cikin 25 sun hade da dan takarar APC a jihar Cross River

- Sun bayyana cewa za su sanya magoya bayansu su zabi Owan-Enoh a zabe mai zuwa

- Owan-Enoh ya mika godiya akan wannan karamci nasu na janye masa ya kuma yi alkawarin cewa ba zai basu kunya ba

Yan takarar kujeran gwamna 16 daga cikin 25 na jam’iyyun siyasa a jihar Cross Rivers a zaben 2019, sun amince da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Sanata John Owan-Enoh a matsayin dan takararsu na hadin gwiwa.

Yan takarar gwamnan sun fito a karkashin kungiyar Coalition of Owan Friends of Political Parties And Groups (COFOPPAG).

An gudanar da bikin amincewar ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu a Calabar inda dukkanin yan takarar suka hallara.

Yanzu Yanzu: Yan takarar gwamna 16 sun lamunce ma dan takarar APC a Cross River

Yanzu Yanzu: Yan takarar gwamna 16 sun lamunce ma dan takarar APC a Cross River
Source: Depositphotos

Sun bayyana cewa za su sanya magoya bayansu su zabi Owan-Enoh a zabe mai zuwa.

Shugaba kungiyar, Mista Charles Okoi ya bayyana cewa sun yanke wannan shawarar ne bayan gani da suka yi cewa Owan-Enoh ya fi cancanta, kuma kasancewarsa dan syasa mai cike da kwarewa sannan mai son kawo ci gaban da ake bukata.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da kwamitoci don zaben 2019

Da yake jawabi, dan takarar gwamnan na APC, Owan-Enoh yace ya gode da wannan karamci nasu na janye masa da suka yi a matsayin dan takara a zabe mai zuwa, ya kuma yi alkawarin cewa ba zai basu kunya ba.

Yace hakan ya matukar taba zuciyarsa yadda suka ajiye banbancin su a gefe sannan suka mara masa baya saboda ci gaban jiharsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel