Matsalar Boko Haram: Ministan tsaro ya dira garin Maiduguri don gane ma idanunsa

Matsalar Boko Haram: Ministan tsaro ya dira garin Maiduguri don gane ma idanunsa

Ministan tsaro, Mansur Dan Ali ya kai ziyara garin Maidugurin jahar Borno sakamakon sabbin hare haren da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram da na IS suke kaiwa a yan kwanakin nan babu kakkautawa.

Minista Dan Ali yace ya kai wannan ziyara ne biyo bayan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi nay a garzaya jahar Borno don duba yadda Sojojin Operation Lafiya Dole ke gudanar da aikinsu, tare da samo masa sahihan bayanai.

KU KARANTA: Mataimakin gwamnan jahar Kano ya yi ram da fitaccen dan jagaliyan siyasa a Kano

Matsalar Boko Haram: Ministan tsaro ya dira garin Maiduguri don gane ma idanunsa

Ministan tsaro
Source: UGC

Haka nan a yayin ziyarar, Dan Ali ya gana da wasu manyan kwamandojin rundunar Sojan kasa dake yaki da kungiyar Boko Haram, daga cikinsu har da babban hafsan sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai da Manjo janar Benson Akinroluyo.

Da yake zantawa da majiyar Legit.com, Dan Ali yace shugaba Buhari na son ya san halin da ake cikin da sabon umarnin daya baiwa Sojoji na game da yaki da yan ta’addan Boko Haram, sa’annan yana bukatar ya san cigaban da aka samu da kuma kalubaken da suke fuskanta domin a warwaresu.

Daga karshe minista Dan Ali yace zai garzaya yankin tafkin Chadi domin game ma idanunsa halin da Sojoji ke ciki a bakin daga tare da kwakulo ma shugaba Buhari bayanai sahihai wanda yake sa ran zasu ilimantar da shi game da matakin daya kamata a dauka a gaba.

A wani labarin kuma, Rundunar sojojin saman Najeriya da yanzu haka ke yaki da 'yan ta'addan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram ta ce wani jirginta mai saukar ungulu ya yi hatsari yayin yaki da yan Boko Haram a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel