Rikicin Benuwe: An kama wani yaro mai shekaru 21 dauke da wayoyin salula 26, bindiga

Rikicin Benuwe: An kama wani yaro mai shekaru 21 dauke da wayoyin salula 26, bindiga

Rundunar Yansandan jahar Benuwe ta bayyana cewa ta kama wani matashi mai karancin shekaru, shekara 21, mai suna Godwin Raphael dauke da samfurin wayoyin salula daban daban guda ashirin da shida, da wata karamar bindiga guda daya.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Yansandan sun kama wannnan mugun matashi ne a karamar hukumar Otukpo ta jahar Benuwe, kamar yadda kaakakin rundunar, DSP Moses Yamu ya bayyana.

KU KARANTA: Mataimakin gwamnan jahar Kano ya yi ram da fitaccen dan jagaliyan siyasa a Kano

Kaakaki Yamu ya bayyana haka ne ga manema labaru a ranar Alhamis 3 ga watan Janairu a babban birnin jahar Benuwe, Makurdi, inda yace jami’an rundunar Yansanda sun samu nasarar cafke Raphael ne a ranar 25 ga watan Disamba, wato ranar kirismeti.

Haka zalika dansanda Yamu yace sun kama Raphael ne bayan sun samu bayanan sirri game da ayyukan miyagun mutane daga wasu igantattun majiyoyi, ya kara da cewa sun kama shi da wayoyin salula 26 samfuri daban daban.

Sauran abubuwan da suka kama a hannun Raphael sun hada da karamar bindigar Fistu, alburusai, da wani babban talabijin na zamani, sai dai kaakaki Yamu yace Raphael yana tare da wasu gagga gaggan miyagun mutane ne, amma sun tsere.

A hannu guda kuma, DSP Yamu yace rundunar Yansandan jahar Benuwe ta kama wasu mutane goma sha daya, dukkaninsu matasa a lokacin da ake kokarin shigar dasu kungiyar asiri a unguwar Wadata dake cikin garin Benuwe a ranar 26 ga watan Disamba.

Bugu da kari a kokarin Yansanda na tsaftace jahar Benuwe daga ayyukan miyagun mutane, rundunar ta kama wasu gungun yan fashi guda hudu a karamar hukumar Ado, tare da kwace mota kirar Corolla, bindiga da alburusai, yan fashin sun hada da Monday Igbo, Moses Abbah, Friday Oguche da Godwin Ochigbo.

Daga karshe kaakakin yace sun sake kama wasu yan kungiyar asiri ta Red Fraternity guda hudu a garin Otukpo a ranar 27 ga watan Disamba, dauke da alburusai, kwalban giya, tabar wiwi da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel