Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da kwamitoci don zaben 2019

Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da kwamitoci don zaben 2019

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar da kwamitoci biyu domin zaben 2019

- Kwamitin farko zai kula da abubuwan da suka shafi dabarun zabe yayinda kwamiti na biyu zai kula da harkokin cikin gida

- Hukumar zaben za ta kuma gana da malaman ASUU a gobe sannan a mako mai zuwa za ta kana da kungiyar kwadago na Najeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da kwamitoci biyu domin tabbatar da an gudanar da zaben 2019 cikin lumana.

An gudanar da taron kaddmarwar a rana Alhamis, 3 ga watan Janairu, a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da kwamitoci don zaben 2019

Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da kwamitoci don zaben 2019
Source: Facebook

Bayan kaddamarwar, shugaban kungiyar, Mahmood Yakubu yace zai gana da kungiyar malaman jami’a (ASUU) a ranar Juma’a, 4 ga watan Janairu a sakatariyar kungiyar domin tattauna yajin aiki kan yadda zai shafi zabe.

Kwamitin farko zai kula da abubuwan da suka shafi dabarun zabe yayinda kwamiti na biyu zai kula da harkokin cikin gida, a cewar Mista Yakubu.

KU KARANTA KUMA: Zan sauka daga kujerar gwamna idan hakan zai dawo da zaman lafiya a Zamfara – Gwamna Yari

Kwamiyin dabarun ya hada da wakilai daga hukumar kula da afkuwar hatsarurruka (FRSC), hukumar kula da shige da fice, rundunar soji, rundunar sojin sama, rundunar sojin ruwa, kwastam, sashin kwararru na yan sandan farin kaya, rundunar yan sanda, da hukumar kula da filayen jiragen sama na Najeriya.

ABM Muazu da yake Magana a madadin kwamitin, ya nuna yabawa ga hukumar kan nauyin da ya rataya a wuyansu, yayinda ya ba shgaban hukumar da kasa tabbacin cewa kwamitin za ta yi duk abunda ake bukata daga gareta domin tabbatar da zabe cikin nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel