2019: Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya koma APC

2019: Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya koma APC

A yayin da ya rage kasa da sati 6 kafin fara zabukan shekarar nan da muke ciki, jam'iyyar adawa ta PDP ta samu koma baya bayan canjin shekar tsohon shugabanta a jihar Neja, Alhaji Abdulrahman Enangi, zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Sai dai a wani martani na gaggawa, jam'iyyar ta PDP ta bayyana cewar ta karbi fiye da matasa dubu uku a karamar hukumar tsohon shugaban nata da ya koma APC.

Enagi, tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Neja na tsawon shekaru 8, ya koma jam'iyyar APC a jiya, Laraba, tare da magoya bayansa fiye da 500.

Da yake jawabi ga dandazon jama'a yayin bikin karbar sa, Enangi ya ce ya koma APC ne domin hada kai da gwamnatin jihar Neja a kokarinta na raya karkara da birane.

2019: Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya koma APC

2019: Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya koma APC
Source: Depositphotos

"Na yanke shawarar komawa jam'iyyar APC ne saboda irin rawar ganin da ta taka a bangaren kawo ribar dimokradiyya ga karamar hukuma ta da ragowar sassan jihar Neja."

"Da yawan matasa zasu canja sheka daga PDP zuwa APC," a kalaman Enangi.

Wannnan shine karo na biyu da Enangi ya fadi zaben cikin gida a jam'iyyar PDP na neman takarar kujerar Sanata.

DUBA WANNAN: Na koma APC ne bayan hira mai dadi da Buhari - Tsohon gwamnan PDP

Da yake jawabi yayin karbar Enangi, Alhaji Suleiman Usman, shugaban jam'iyyar APC na karamar hukuma, ya bayyana canjin shekar tsohon shugaban jam'iyyar a matsayin abun alheri.

"Mun gama shirin cin zabe a matakin karamar hukuma, sanatoriya, jiha, da ma tarayya," a kalaman Usman.

Kazalika a nasu bangaren, matasan da suka canja sheka zuwa PDP karkashin jagorancin Sarkin matasan Enangi, sun ce sun fita daga APC ne saboda dawowar tsohon shugaban PDP cikinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel