Dakaru sun fi mayakan Boko Haram nagartattun Makamai - Hukumar Sojin Kasa

Dakaru sun fi mayakan Boko Haram nagartattun Makamai - Hukumar Sojin Kasa

- Hukumar sojin kasa ta Najeriya ta karyata zargin cewa makamai na mayakan Boko Haram sun yiwa na dakarunta zarra ta fuskar nagarta da inganci

- Kakakin Soji Janar Kukasheka ya ce masu da'awar wannan lamari makaryata na da ba bu kishin kasa a zukatan su

- Birgediya Janar Kukasheka ya yi gargadin cewa yaduwar wannan farfaganda na jefa fargaba a zukatan dakarun soji

Hukumar Sojin kasa ta Najeriya ta yi watsi da abinda ta kiraye shi a matasayin karairayi da zantuka na shaci fadi dake faman yaduwa kan cewa mayakan boko haram sun yiwa dakarunta fintinkau ta fuskar mallakar ingatattun da nagartattun makaman yaki.

Hukumar sojin kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito ta bayyana cewa, wannan lamari shafa labari shuni ne kurum da ba su da wani tushe ballantana madogara illa iyaka manufa ta yada farfaganda ta jefa fargaba a zukatan dakarunta.

Dakaru sun fi mayakan Boko Haram nagartattun Makamai - Hukumar Sojin Kasa

Dakaru sun fi mayakan Boko Haram nagartattun Makamai - Hukumar Sojin Kasa
Source: Depositphotos

Kakakin hukumar sojin, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman, shine ya bayar da shaidar hakan cikin wasu jawabai da ya gabatar na karin haske dangane da ababe da suka shafi yaki da ta'addanci a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Janar Kukasheka ya ke cewa, ababe da suka shafi al'amurran dakarun soji ba su da wata alaka ko dangantaka ta kusa ko ta nesa da gasa ta kowace fuska. Ya bayyana takaicin sa dangane da yadda siyasa da son zuciya suka mamaye duj wata gudanarwar su da yunkuri na yaki da ta'addanci.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya gana da Kungiyar daliban Najeriya kan yajin aikin ASUU

Babban jami'in sojin ya jaddada cewa, yada karairayi da zantuka na shaci fadi kan hukumar sojin ba su da wata manufa illa iyaka son zuciya da kuma dalilai na siyasa da marasa kishin kasa suka ara kuma suka yafa.

Kazalika ya kara da cewa, yada wannan mummunanr farfaganda ba ta takaita kadai a iyakokin kasar nan ba, da tasirinta ya sanya masu tayar da kayar baya na Boko Haram suka zartar da wasu munanan hare-hare akan dakaru a kwana-kwanan nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel